Atiku Abubakar ya yi wa Obaseki barka da zuwa PDP

Atiku Abubakar ya yi wa Obaseki barka da zuwa PDP

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar, ya taya Gwamna Godwin Obaseki murnar komawa jam'iyyar PDP.

A wata takarda da mai magana da yawun Atiku, Paul Ebe, ya sa hannu a ranar Juma'a, ya yi maraba da Gwamna Obaseki zuwa jam'iyyar PDP.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana karfin guiwar cewa zai zama zabi nagari ga jama'ar jihar Edo, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Dan takarar shugabancin kasar a zaben 2019 ya tabbatar da cewa, Gwamnan Obaseki ya koma jam'iyyar PDP ne a lokacin da ta shirya bada shugabanci nagari ga jama'ar Najeriya baki daya.

"Ina farin ciki tare da taya ka murnar dawowa haske. Barka da barin jam'iyyar kangi sannan ka dawo ta gaskiyar damokaradiyya a Najeriya.

"Babu shakka dawowarka PDP zai karfafa jam'iyyar ta yadda mutane za su gano dalilin damokaradiyya a kasar nan tare da dawo da martabar jama'a.

"Jam'iyyar PDP da ka dawo a yau ta riga ta sauya tsari. Wacce har abada za ta kasance jam'iyyar jama'a saboda jama'a.

"Ina da tabbacin cewa dawowarka jam'iyyar nan babban jari ce kuma kai kanka kadara ne ga PDP.

"A tare za mu hada kai wurin tabbatar da mun kawar da duka wani nau'in mulkin kama-karya tare da tabbatar da shugabanci nagari a jihar Edo da Najeriya baki daya," Atiku yace.

Atiku Abubakar ya yi wa Obaseki barka da zuwa PDP
Atiku Abubakar ya yi wa Obaseki barka da zuwa PDP. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da ɗumi-ɗumi: 'Yan bindiga sun sake sace mahaifin tsohon gwamnan APC, Joshua Dariye

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP a yau Juma’a 19 ga watan Yuni, 2020, Legit Hausa ta samu rahoto.

Gwamna ya alanta sauya shekarsa ne a hedkwatan jam'iyyar PDP ta jihar Edo da ke `Benin City, abbar birnn jihar ranan nan.

Ya ce yana da masaniyar nauyin da ya hau kansa yanzu da ya koma jam'iyyar saboda daga yanzu shine uban dukkan 'yayan jam'iyyar a Edo.

Ya ce ba tare da bata lokaci ba, zai garzaya rijista bisa ka'ida a matsayin sabon dan jam'iyya. Gwamna Obaseki ya samu rakiyar dimbin mabiya da masoyansa.

Gwamnan da kansa ya bayyana hakan a shafin na Twitter inda yace: "Na sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP domin cigaba da manufata na saken takaran neman kujeran gwamnan jihar Edo."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel