Da ɗumi-ɗumi: 'Yan bindiga sun sake sace mahaifin tsohon gwamnan APC, Joshua Dariye

Da ɗumi-ɗumi: 'Yan bindiga sun sake sace mahaifin tsohon gwamnan APC, Joshua Dariye

Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun sake sace mahaifin tsohon gwamnan jihar Plateau, Joshua Dariye.

A bayan an taba sace Pa Defwan Dariye a watan Fabrairun 2015 a gidansa da ke Mushere, a karamar hukumar Bokkos na jihar.

'Yan banga sun ceto sa bayan kwanaki kadan a kan iyakar jihar Nasarwa da Plateau.

A wannan karon na biyu, an gano cewa 'yan bindigan sun tafi gidansa da ke garin Mushere kuma suka yi awon gaba da shi zuwa wani wurin da babu wanda ya sani.

Da ɗumi-ɗumi: 'Yan bindiga sun sake sace mahaifin Dariye
Da ɗumi-ɗumi: 'Yan bindiga sun sake sace mahaifin Dariye. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

Wani mazaunin garin, Bulus Gambo ya tabbatarwa The Punch sace mahaifin tsohon gwamnan a Jos a ranar Juma'a.

Gambo ya ce, "Labarin gaskiya ne. Abin ya faru a safiyar ranar Alhamis. Dattijon na zaune a gidansa kwatsam wasu yan bindiga suka zo suka yi awon gaba da shi."

Wani ma'aikacin shugaban karamar hukumar Bokkos, Magit Mangut Mafiyai shima ya tabbatar da sace Pa Dariye.

DUBA WANNAN: Sakon Sultan ga Buhari: Ƴan Najeriya na da ikon yin zanga-zanga kan tsaro

Mafiyai ya ce shugaban karamar hukumar, Yusuf Mahanan Machen ya ziyarci gidan Pa Dariye kuma ya umurci jami'an tsaro suyi duk mai yiwuwa domin ceto shi.

Kakakin 'yan sandan jihar Plateau, Ubah Ogaba ya ce an aika da jami'an tsaro karamar hukumar domin suyi farauatar wadanda suka sace Pa Dariye tare da ceto shi.

Ya ce, "A lokacin da aka sanar da mu abinda ya faru, kwamishinan 'yan sanda ya jagoranci wasu jami'ai zuwa Bokkos. Twagan jami'an tsaron da aka umurci su ceto shi sun fara aiki, muna fatan za su ceto shi."

Dan wanda aka sace kuma tsohon gwamnan jihar, Joshua Dariye a halin yanzu yana gidan yari inda ya ke zaman shekara 10 bayan samunsa da laifin cin amana yayin da ya ke gwamna daga 1999 zuwa 2007.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel