Za a 'feshe' Majalisar Kaduna bayan wani ma'aikaci ya kamu da korona

Za a 'feshe' Majalisar Kaduna bayan wani ma'aikaci ya kamu da korona

Za ayi feshin magani a Majalisar Jihar Kaduna bayan wani ma'aikacin majalisar ya kamu da COVID-19 a ranar Laraba kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa wakilinta ya ga ababen hawa a harabar majalisar a ranar Laraba da safiyar Alhamis amma ba a bari ya shiga ba duk da cewa akwai mutane kalilan cikin majalisar.

Wani ma'aikacin majalisar ya bayyana cewa an umurci dukkan wadanda suka yi cudanya da wanda ya kamu da cutar su killace kansu yayinda aka dauki samfuri daga jikinsu don gwaji.

Za a 'feshe' Majalisar Kaduna bayan wani ma'aikaci ya kamu da korona
Za a 'feshe' Majalisar Kaduna bayan wani ma'aikaci ya kamu da korona. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Karin mutum 745 sun kamu da korona a Najeriya

Shugaban Kwamitin Ilimi na majalisar, wanda kuma shine mataimakin shugaban kwamitin lafiya, Hon. Suleiman Dabo mai wakiltan Zaria city ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa kwamitin lafiya ta san da batun.

Ya ce: "Daya daga cikin ma'aikatan majalisar daga ofishin akawun majalisar ya kamu da coronavirus kuma an dauki samfurin wadanda ke aiki tare da shi domin yin gwaji."

A makon da ta gabata ne dai aka yi bata-kashi a majalisar a ranar Alhamis yayin da mambobi 24 cikin 34 suka tsige mataimakin kakakin majalisar Hon. Mukhtar Isa Hazo.

A wani labarin, kun ji cewa an kwantar da Shugaba Juan Orlando Hernandez na kasar Honduras a asibiti a babban birnin kasar ta Tegucigalpa bayan an sanar da cewa ya kamu da coronavirus a ranar Laraba.

Likitocin da suka duba shugaban kasar sun ce sakamakon binciken da aka yi masa ya nuna yana fama da ciwon pneumonia kamar yadda kakakin gwamnati, Francis Contreras ya shaidawa manema labarai.

Ya kara da cewa, "akwai wasu kwayoyin cuta da suka shiga huhun Hernandez amma yana cikin koshin lafiya."

Shugaban kasar mai shekara 51 a ranar Talata ya sanar da cewa baya jin dadin jikinsa kuma a karshen mako aka gano cewa kwayar cutar COVID-19 ce.

Sanarwar da gwamnatin ta fitar ya ce, "Hernandez yana kiyaye dukkan matakan kare kansa daga cutar da hukumomin lafiya suka bayar amma saboda yanayin aikinsa yana da wahala dena cudanya da mutane."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel