'Yan bindiga sun kashe mahaifin mai neman takarar gwamna a Edo a APC

'Yan bindiga sun kashe mahaifin mai neman takarar gwamna a Edo a APC

'Yan bindiga a ranar Alhamis sun kashe malamin jami'a mai shekara 80, Farfesa Christopher Ogiehor, mahaifin mai neman takarar gwamna a karkashin jami'yyar APC a jihar Edo, Mathew Iduoriyekemwen.

The Punch ta ruwaito cewa an tsinci gawar Ogiehor ne a gidansa da ke lamba 13 layin Egbor Anenne daura da Benoni kusa da rukunin gidajen gwamnati da ke binrin Benin.

Wani daga cikin iyalansa da ya nemi a boye sunansa ya yi bayanin cewa an tsinci dattijon kwance cikin jininsa a safiyar ranar Alhamis.

'Yan bindiga sun kashe mahaifin mai neman takarar gwamnan a Edo a APC
'Yan bindiga sun kashe mahaifin mai neman takarar gwamnan a Edo a APC. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Mataimakin shugaban APC ya yi watsi da sabuwar umurnin kotu

"An tsinci gawarsa cikin dakinsa da rauni a kansa kuma hannunsa a daure a bayansa, wanda hakan alama ne da ke nuna an buga masa wani abu a kansa ko kuma an sheke shi.

"Jami'an 'yan sanda daga sashin binciken laifuka sun isa gidansa a safiyar yau domin fara bincike. Ba za mu iya cewa ga wanda ya aikata wannan mummun abin ba," in ji majiyar iyalin.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, Chidi Nwabuzor ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce jami'ai daga sashin binciken kisa sun tafi gidan marigayin don daukan bayanai.

A wani labarin daban, kun ji cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta saki fursunoni 6,590 da ke tsare a gidajen gyaran hali daban daban a sassar kasar.

Hakan na kunshe ne cikin wani rubutu da Attoney Janar na kasa, AGF, kuma ministan Shari'a, Abubakar Malami, SAN, ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Laraba 17 ga watan Yuni.

A cewar Malami, fursunonin sun cika ka'idojin da aka gindaya na sakin fursunoni daga gidajen gyaran hali 32.

Ministan yayin da ya ke gabatar da nasarorin da ma'aikatarsa ta samu daga 2015 zuwa 2020 ya ce ya taka muhimmiyar rawa wurin ganin an rage cinkoso a gidajen gyaran hali a wasu jihohi 14.

Idan za a iya tunawa, Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci a bullo da hanyoyin gaggauta sharia da rage cinkosu a gidajen gyaran hali a kasar sakamakon bullar annobar coronavirus.

Fadar shugaban kasar ta bakin mashawarcin shugaban kasa na musamman kan kafafen watsa labarai, Femi Adesina ne ya bayyana hakan a ranar Laraba 22 ga watan Afrilu.

Shugaban na Najeriya a wasikar da ya aike wa Alkalin Alkalan Najeriya, Tanko Muhammad ya tunatar da shi rokon da Majalisar Dinkin Duniya ta yi ga kasashe su rage cinkoso a gidajen gyran hali na kasashensu don samar da tazara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel