Karin mutum 745 sun kamu da korona a Najeriya

Karin mutum 745 sun kamu da korona a Najeriya

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 745 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11.43 na daren ranar Alhamis 18 ga Yuni na shekarar 2020.

Karin mutum 745 sun kamu da korona a Najeriya
Karin mutum 745 sun kamu da korona a Najeriya. Hoto daga New Zandar
Asali: UGC

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 745 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

Lagos-280

Oyo-103

Ebonyi-72

FCT-60

Imo-46

Edo-34

Delta-33

Rivers-25

Kaduna-23

Ondo-16

Katsina-12

Kano-10

DUBA WANNAN: Sakon Sultan ga Buhari: Ƴan Najeriya na da ikon yin zanga-zanga kan tsaro

Bauchi-8

Borno-7

Kwara-5

Gombe-4

Sokoto-2

Enugu-2

Yobe-1

Osun-1

Nasarawa-1

Alkalluman da hukumar ta dakile cututtukan ta fitar a ranar Alhamis 18 ga Yunin shekarar 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar ta korona a kasar 18,480.

An sallami mutum 6307 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 475.

A wani labarin, kun ji cewa an kwantar da Shugaba Juan Orlando Hernandez na kasar Honduras a asibiti a babban birnin kasar ta Tegucigalpa bayan an sanar da cewa ya kamu da coronavirus a ranar Laraba.

Likitocin da suka duba shugaban kasar sun ce sakamakon binciken da aka yi masa ya nuna yana fama da ciwon pneumonia kamar yadda kakakin gwamnati, Francis Contreras ya shaidawa manema labarai.

Ya kara da cewa, "akwai wasu kwayoyin cuta da suka shiga huhun Hernandez amma yana cikin koshin lafiya."

Shugaban kasar mai shekara 51 a ranar Talata ya sanar da cewa baya jin dadin jikinsa kuma a karshen mako aka gano cewa kwayar cutar COVID-19 ce.

Sanarwar da gwamnatin ta fitar ya ce, "Hernandez yana kiyaye dukkan matakan kare kansa daga cutar da hukumomin lafiya suka bayar amma saboda yanayin aikinsa yana da wahala dena cudanya da mutane."

Matarsa, Ana Garcia ita ma ta kamu da kwayar cutar ta coronavirus amma a halin yanzu ba ta da alamomin cutar a cewar jamian gwamnatin kasar.

Honduras na cikin kasashen duniya da annobar ta coronavirus ta yi wa illa sosai inda mutane da yawa a biranen Tegucigalpa da San Pedro Sula suka kamu da cutar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel