Hajjin 2020: Maniyyatan Nijar ba za suyi aikin Hajjin bana ba

Hajjin 2020: Maniyyatan Nijar ba za suyi aikin Hajjin bana ba

Gwamnatin Jamhuriyar kasar Nijar ta shiga jerin kasashen da suka dauki matakin cewa ba za su je Aikin Hajjin bana ba domin annobar cutar coronavirus.

Nijar ta cimma wannan matsaya ne bayan ganawa da masu ruwa da tsaki a kan sha'anin Hajji da Umara don sanar da su matsayar da ta cimma game da tafiya hajjin shekarar 2020 a ranar Alhamis.

Kasar ta ce an dauki wannan matakin ne bayan nazarin sharuddan da hukumomin kasar Saudiyya suka gindaya a kasar domin dakile yaduwar cutar ta coronavirus kamar yadda BBC ta ruwaito.

Gwamnatin ta yi kira ga masu kamfanonin jigilar maniyyata da su daina amsar kudin mutane, su kuma biya basussukan da ake binsu.

Hajjin 2020: Maniyattan Nijar ba za su yi aikin Hajjin bana ba
Hajjin 2020: Maniyattan Nijar ba za su yi aikin Hajjin bana ba. Hoto daga Virtual Mosque
Asali: UGC

Kawo yanzu dai kasar ta Saudiyya ba ta bayyana matakin da ta dauka ba dangane da yiwuwar yin aikin Hajjin na bana.

Amma a ranar Lahadi 14 ga watan Yuni ministan harkokin addini na Saudiyya, Sahibzada Noor-ul-Haq Qadri ya ce ranar Litinin 15 ga watan Yuni kasar za ta yanke shawara ta kashe game da yiwuwar hajjin na 2020.

Sai dai har yanzu ba ta bayyana matsayar ta game da aikin hajjin ba.

DUBA WANNAN: Sakon Sultan ga Buhari: Ƴan Najeriya na da ikon yin zanga-zanga kan tsaro

A wani labari da Legit.ng ta wallafa, kun ji cewa kasar Brunei a ranar Laraba ta sanar da cewa yan kasarta ba za su samu ikon zuwa kasar Saudiyya ba domin yin aikin hajji ba a bana saboda COVID-19 a cewar wata kafar watsa labarai na kasar.

Yayin taron manema labarai, Ministan harkokin addini na kasar, Awang Baddarudin Othman ya ce kasar ba za ta aike da maniyattan ta 1,000 da ta saba daukan dawainiyarsu duk shekara ba kamar yadda Borneo Bulletin ya ruwaito.

Baddarudin ya ce an cimma wannan matsayar ne bayan Sultan Hassanal Bolkiah ya amince da shawarwarin da Cibiyar addinin musulunci ta Brunei ta bayar bayan taron da ta yi ranar Asabar da ta gabata inda ta soke daukan nauyin maniyattan bana.

Brunei ta zama kasa ta hudu a yankin Kudu maso Gabashin Asia da ta ce ba za tayi aikin hajji ba wannan shekarar bayan Singapore, Indonesia da Malaysia.

A watan Mayu, Singapore ta sanar da cewa yan kasar ta ba za suyi aikin hajjin bana ba saboda annobar coronavirus kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A cewar Cibiyar harkokin addinin musulunci ta Singapore, maniyatta 900 da suka biya kudin kujerar zuwa aikin hajjin za su hakura sai shekarar 2021.

Ministan Harkokin Addini na Indonesia, Fachrul Razi, shima ya soke zuwa aikin hajjin na bana saboda fargabar annobar ta korona.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel