Mataimakin shugaban APC ya yi watsi da sabuwar umurnin kotu

Mataimakin shugaban APC ya yi watsi da sabuwar umurnin kotu

Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na shiyar Arewa maso Gabas, Mustapha Salihu ya nesanta kansa daga sabon umurnin da kotu ta bayar da umurtar shi ya kama aiki a matsayin sakataren jamiyyar na kasa.

Salihu ya shaidawa manema labarai a ranar Alhamis a Abuja cewa ba zai yi wu ya bi umurnin ba saboda ya saba matakin da jam'iyyar ta dauka yayin taron shiyoyi da aka gudanar inda aka nada Waziri a matsayin sakaren jam'iyyar na kasa.

Mataimakin shugaban APC ya yi watsi da sabuwar umurnin kotu
Mataimakin shugaban APC ya yi watsi da sabuwar umurnin kotu. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

Sallihu ya ce, "Shiyya ta, Arewa maso Gabas ta zabi Waziri Bulama a matsayin mukadashin sakatare a gaban shugaban Majalisar Dattijai, gwamnonin APC da wasu masu ruwa da tsaki.

"Ina wurin taron a lokacin da aka dauki wannan matakin. Saboda haka mene zai sa in koma in bi umurnin kotu na kama aiki a matsayin sakataren jam'iyya na kasa?

DUBA WANNAN: Sakon Sultan ga Buhari: Ƴan Najeriya na da ikon yin zanga-zanga kan tsaro

"Ba da ni za ayi wannan tabargazan ba. Ba hali ne bane yin irin wannan mumunan siyasar kuma na yi tir da wadanda suka aikata wannan abin.

"A irin wannan lokacin da jam'iyyar ke fama da wata babban kalubale, kamata ya yi duk masu kaunar jam'iyya su hada kai wuri guda don tafiyar da jam'iyyar."

Kamar yadda The Punch ta ruwaito, akwai takardar karar kotu mai kwanan wata 16 ga watan Yunin 2020 da aka shigar a babban kotun Abuja da ke Maitama karkashin mai shari'a S.U. Bature.

Takardan ta nuna cewa wani "Comrade Salihu" ne ya shigar da karar na neman kotu ta bayar da umurnin bashi izinin fara aiki a matsayin sakataren jam'iyya na kasa kafin lokacin da kwamitin kotu za ta yanke hukunci kan lamarin.

Wani Obinna Ugwu ne ya yi rantsuwa a matsayin sheda yayin shigar da karar mai lamba FCT/HC/M/7707/2020.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel