Akwai ƙananan hukumomi 5 a hannun Boko Haram; Ƙusa a gwamnatin Borno ya gyara kuskuren da Buhari ya yi a jawabinsa

Akwai ƙananan hukumomi 5 a hannun Boko Haram; Ƙusa a gwamnatin Borno ya gyara kuskuren da Buhari ya yi a jawabinsa

Mustapha Gubio, Kwamishina mai kulawa da wadanda iftila'i ya fada musu na jihar Borno, ya ce har yanzu akwai a kalla kananan hukumomi 5 cikin 27 da 'yan ta'adda suka mamaye akasin ikirarin da Shugaba Buhari ya yi a jawabinsa na ranar Demokradiyya.

A jawabinsa na bikin ranar Demokradiyya a ranar Juma'a 12 ga watan Yunin 2020, Buhari ya ce baya ga karya lagwan 'yan ta'adda da sojoji su kayi, babu ko karamar hukuma daya a karkashin ikon 'yan ta'adda.

Shugaban kasar ya ce, "An dade da kwato dukkan kananan hukumomin da yan Boko Haram suka mamaye a jihohin Borno, Yobe da Adamawa kuma mazauna garuruwan sun koma gida suna rayuwarsu."

Akwai ƙananan hukumomi 5 a hannun Boko Haram; Ƙusa a gwamnatin Borno ya gyara kuskuren da Buhari ya yi a jawabinsa
Akwai ƙananan hukumomi 5 a hannun Boko Haram; Ƙusa a gwamnatin Borno ya gyara kuskuren da Buhari ya yi a jawabinsa. Hoto daga sarahifidon.com
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Sakon Sultan ga Buhari: Ƴan Najeriya na da ikon yin zanga-zanga kan tsaro

Amma Gubio yayin jawabin da ya yi wa manema labarai a Maiduguri ya ce har yanzu akwai kananan hukumomi biyar da ba su shiguwa saboda yan taada sun samu gindin zama kamar yadda Hum Angle ta ruwaito.

Kananan hukumomin da ya lissafa sun hada da Guzamala, Kukawa, Abadam, Marte da Abadam.

Kwamishinan ya ce, "A karamar hukumar Guzamala, an lalata sansanin sojoji kuma jami'an tsaron sun bar sansanin. Ba za mu iya zuwa Guzamala yin aiki ba har sai an samu jami'an tsaro.

"A watan Mayu, mun kai block 50, 000 Guzamala don fara aiki amma mun dakata saboda rashin tsaro."

Ya cigaba da garin Abidam da Boko Haram suka lalata shima baya shiguwa duba da cewa hanyar garin ba shi da kyau.

Ba bu hanyan shiga garin, Zai yi wahala a fara aikin gine gine kuma idan za a shiga garin sai an bi ta Jamhuriyar Nijar, in ji Kwamishinan.

"Shi kuma karamar hukumar Kukawa dama babu sojoji tun watan Mayu. A yanzu babu ko mutum daya a Kukawa," a cewar Gubio.

Ya kara da cewa, "Gwamna na shirin zuwa Baga, babban garin da ke karamar hukumar Kukawa domin duba barnar da aka yi.

"Barnar da aka yi a Kukawa ba za tayi yawa ba sosai duba da cewa mutane sun dade da yin kaura daga garin, gidaje da sauran gine gine sun fara lalacewa da kansu."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel