Yanzu-yanzu: Jami'an tsaro sun saki shugaban matasan Arewa, Nastura Ashir

Yanzu-yanzu: Jami'an tsaro sun saki shugaban matasan Arewa, Nastura Ashir

Jami'an tsaro a birnin tarayya Abuja sun saki shugaban gamayyar kungiyoyin matasan Arewa wato CNG, Alhaji Nasturah Ashir Sherrif, bayan kwana biyu a hannun hukuma.

An damke Sharrifa ne ranar Talata kuma aka garzaya da shi Abuja bayan zanga-zangan lumana a jihar Katsina kan kisan kiyashin da ake yiwa yan Arewacin Najeriya.

Daily Nigerian ta samu jawabin kakakin gamayyar kungiyoyin Arewa CNG, AbdulAzeez Sulaiman, inda ya tabbatar da sakin Nastura.

Yace: "Muna masu tabbatar da muku cewa an saki Sharif ne saboda irin jajircewan da kungiyar CNG, kungiyar dattawan Arewa, manyan shugabanni da dattawa a Arewa, wani sashen kungiyoyin fafutuka da kuma lurar kafafen yada labarai a gida da waje."

"Hakazalika muna masu godiya bisa taimako, goyon baya da hakurin al'ummar Arewa cikin wannan lokaci da aka garkame Shariff. Hakan ya kara mana karfin gwiwa."

"Muna tabbatarwa al'umma cewa ba zamu gaji ba wajen fafutukarmu na samun rayuwa mai adalci da inganci ko ta yaya ne."

Yanzu-yanzu: Jami'an tsaro sun saki shugaban matasan Arewa, Nastura Ashir
Yanzu-yanzu: Jami'an tsaro sun saki shugaban matasan Arewa, Nastura Ashir
Asali: Facebook

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel