Yanzu-yanzu: Kotu ta tabbatar da Giadom a matsayin shugaban APC na kasa
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta tabbatar da Victor Giadom a matsayin mukaddashin shugaban jam'iyyar APC na kasa.
Kotun ta yanke hukuncin cewa Mustapha Salihu, mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa a yankin arewa maso gabas da ya zama sakataren jam'iyyar na kasa.
Hukuncin kotun na zuwa ne a ranar Alhamis bayan korafin da Salihu ya shigar a gabanta.
Alkalin kotun, S. U Bature, ya tabbatar da cewa hukuncin zai ci gaba da aiki har zuwa lokacin da jam'iyyar za ta yi a taron shugabanninta na kasa.
Hukuncin zai yi aiki na makonni biyu ne ko kuma a sabunta sa.
Jam'iyyar ta rincabe da rikici a tsakanin shugabanninta bayan da kotun daukaka kara ta jaddada dakatar da Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam'iyyar na kasa.
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke hukuncin dakatar da Oshiomhole a matsayin shugaban jam'iyyar APC na kasa a watan Maris 2020.

Asali: UGC
KU KARANTA: Yadda za a shawo kan matsalar 'yan bindiga a Katsina - Shugaban manoma
Yayin sanar da Abiola Ajimobi, tsohon gwamnan jihar Oyo a matsayin mukaddashin shugaban jam'iyyar na kasa, Giadom ya bayyana kansa a matsayin shugaban jam'iyyar.
Giadom ya soke hukuncin hana Godwin Obaseki fitowa takarar gwamnan jihar Oyo a zaben fidda gwanin da za a yi a ranar 22 ga watan Yunin 2020 tare da umartar sabuwar tantancewa.
Amma kuma 'yan kwamitin gudanar da ayyuka na jam'iyyar masu biyayya ga Ajimobi sun zabi Hilliard Eta, mataimakin shugaban jam'iyyar APC na yankin kudu-kudu da ya maye gurbin Ajimobi saboda rashin lafiyarsa.
Bature ne alkalin da ya bada umarnin maye gurbin Giadom da Oshiomhole a watan Maris a matsayin shugaban jam'iyyar na kasa.
A lokacin da aka tuntubi Salihu, ya sanar da The Cable cewa ya matukar shan mamaki a kan hukuncin kotun don shi ya yi gaba.
Amma Salihu bai amsa tambayoyin da aka masa ba na cewa ko ya janye korafinsa ko kuwa.
Rikici ya rincabe a tsakanin shugabannin jam'iyyar tuna bayan dakatar da Adams Oshiomhole da kotun daukaka kara tayi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng