Gwamnatin Kano ta haramta goyo a babur, ta bayyana dalili
Gwamnatin jihar Kano ta sanar da daukan matakin haramta goyo a kan babur mai kafa biyu a ilahirin fadin jihar.
Baffa Babba Dan Agundi, shugaban hukumar kula da zirga - zirgar ababen hawa a Kano (KAROTA), ya kare gwamnatin jihar Kano a kan daukan wannan mataki.
Yayin hirarsa da BBC, Baffa ya ce gwamnati ta dauki matakin ne saboda wasu mutane na kokarin dawo da sana'ar acaba a jihar.
A cewarsa, dokar, ta hana goyo a babur, za ta faera aiki ne daga ranar Alhamis, 18 ga watan Yuni.
Da ya ke mayar da martani ga masu amfani da babura domin saukakawa kansu sufuri, Baffa ya ce gwamnati ba ta dauki matakin domin muzgunawa jama'a ba, sai don magance matsalar da ake fuskanta ta shigowa da mutane cikin Kano ta barauniyar hanya.
Ma su amfani da babura a jihar sun nuna rashin jin dadinsu a kan matakin da gwamnati ta dauka.
A cewar Baffa, gwamnati ta dauki matakin ne domin karfafa dokar tarayya ta hana bulaguro zuwa jihohi saboda dakile yaduwar annobar korona.

Asali: Facebook
Gwamnatin Kano, lokacin mulkin tsohon gwamna, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ta fara haramta sana'ar acaba a shekarar 2013.
DUBA WANNAN: Fayose ya bayyana abinda ya haifarwa da jam'iyyar APC rikici
Ta dauki matakin ne yayin da hare - haren mayakan kungiyar Boko Haram suka yawaita a jihar a wancan lokacin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng