Daukan sabbin ma'aikata: Babban kwamandan NSCDC ya bayyana halin da ake ciki

Daukan sabbin ma'aikata: Babban kwamandan NSCDC ya bayyana halin da ake ciki

Babban kwamandan rundunar tsaro ta NSCDC (Nigeria Security and Civil Defence Corps), Abdullahi Gana Muhammadu, ya ce an dakatar da batun daukan sabbin ma'aikata har zuwa sanarwa ta gaba.

Kwamandan ya sanar da hakan ne ranar Alhamis a cikin wani jawabi da kakakinsa, Ekunola Gbenga, ya fitar.

Shugaban rundunar tsaron ya ce 'yan damfara suna aikawa jama'a sakon gayyatarsu zuwa tantancewa da bayar da horo.

"An ankarar da rundunar tsaro ta NSCDC a kan al'amuran wasu 'yan damfara da ke zambatar mutane ta hanyar aika musu sakon waya ko ta dandalin sada zumunta domin gayyatarsu zuwa tantancewa ko bukatar ganawa dasu dangane da aikin da suke nema da NSCDC.

"Rundunar tsaro ta NSCDC ta bawa kiyaye lafiyar jama'a fifiko, a saboda haka muna biyayya ga gwamnati da kuma shawarwarin da take bayarwa domin dakile yaduwar annobar korona a fadin kasa.

"Domin tabbatar da cewa ba mu saka kowa cikin hatsarin kamuwa da kwayar cutar korona ba, mun dakatar da batun daukan sabbin ma'aikata, amma sunayen da aka fitar suna nan daram, ba sauyi," a cewar sanarwar.

Daukan sabbin ma'aikata: Babban kwamandan NSCDC ya bayyana halin da ake ciki
Jami'an NSCDC
Asali: UGC

NSCDC ta jaddada cewa a halin yanzu ba ta gudanar da wata tantancewa kuma ba ta aika sakon gayyatar ganawa da masu neman aiki ba.

DUBA WANNAN: An kori janar a rundunar sojin Najeriya 'babu girma, babu arziki'

Rundunar tsaron ta bayyana cewa duk lokacin da bukatar hakan ta taso za ta fitar da sanarwa ga jama'a a shafinta na yanar gizo: www.nscdc.gov.ng da da sauran shafukan sada zumunta na rundunar da kuma manyan jaridu na kasar nan.

A cewar NSCDC, rundunar ba ta da wasu dillalai ko wakilai da suke yi mata aiki, a saboda haka, ta yi kira ga masu neman aiki su kai rahoton duk wanda ya nemi wani abu a hannunsu da sunan wakilinta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel