Kunyi kasa a gwiwa, ba zan sake daukan wani uzuri ba - Buhari ga Hafsoshin tsaro

Kunyi kasa a gwiwa, ba zan sake daukan wani uzuri ba - Buhari ga Hafsoshin tsaro

Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna bacin ransa kan yadda lamarin tsaro ya tabarbare a kasar yan kwanakin nan, The Nation ta rahoto.

Hakan ya bayyana ne daga bakin Mai bada shawara kan lamuran tsaro NSA, Manjo Janar Babagana Munguno (mai murabus), bayan zamansu da shugaban kasan.

Munguno ya bayyanawa manema labaran fadar shugaban kasa cewa shugaban kasan ya bukaci hafsoshin tsaro su kara kaimi wajen shawo kan matsalar tsaro.

A cewarsa, shugaba Buhari yace, duk da cewa hafsoshin tsaron na iyakan kokarinsu, da alamun sun yi kasa a gwiwa wajen fuskantar matsalar tsaron da ta zaman babban kalubale.

Saboda haka ya ce ba zai sake daukan wani uzuri daga garesu ba kuma kowa yayi abinda ya kamata.

Bayan haka, shugaba Buhari ya nuna bacin ransa kan rashin hadin kai tsakanin hukumomin tsaro. Ya yi kira da su hada karfi da karfe wajen magance matsalar tsaro a Najeriya.

Hakazalika, ya yi kira ga ofishin NSA ya hadu da gwamnonin jihohin yankin Arewa maso yamma da gwamnan jihar Neja kan yadda aka shirya durfafan yan bindiga da yankunanasu.

KU KARANTA: Ma'aikatan lafiya 29 sun kamu da COVID-19 a Plateau

Kunyi kasa a gwiwa, ba zan sake daukan wani uzuri ba - Buhari ga Hafsoshin tsaro
Kunyi kasa a gwiwa, ba zan sake daukan wani uzuri ba - Buhari ga Hafsoshin tsaro
Asali: Twitter

Mun kawo muku rahoton cewa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya shiga ganawa da manyan hafsoshin tsaro da safiyar Alhamis, 18 ga Yuni, 2020 a fadarsa dake Aso Villa Abuja.

Hadimin Buhari, Bashir Ahmad, ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita.

Hafsoshin tsaron sun dira fadar shugaban kasa ne karkashin jagorancin shugaban dukkan sassan sojojin Najeriya, Janar Gabriel Olonisakin.

Daga cikin wadanda suka halarci zaman sune Also at the meeting were the ,Manjo Janar Babagana Monguno (rtd); Ministan tsaro, Birgediya Janar Bashir Salihi Magashi (rtd); sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa., Farfesa Ibrahim Gambari.

Wannan zaman ya zo kwana daya bayan gwamnatin kasar Amurka ta nuna damuwarta kan irin kisan kiyashin da ake yiwa yan Arewacin Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel