Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari ya shiga ganawar sirri da hafsoshin tsaro

Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari ya shiga ganawar sirri da hafsoshin tsaro

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga ganawa da manyan hafsoshin tsaro da safiyar Alhamis, 18 ga Yuni, 2020 a fadarsa dake Aso Villa Abuja.

Hadimin Buhari, Bashir Ahmad, ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita.

Hafsoshin tsaron sun dira fadar shugaban kasa ne karkashin jagorancin shugaban dukkan sassan sojojin Najeriya, Janar Gabriel Olonisakin.

Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari ya shiga ganawar sirri da hafsoshin tsaro
Shugaba Muhammadu Buhari ya shiga ganawar sirri da hafsoshin tsaro
Asali: Twitter

Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari ya shiga ganawar sirri da hafsoshin tsaro
Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari ya shiga ganawar sirri da hafsoshin tsaro
Asali: Twitter

Wannan zaman ya zo kwana daya bayan gwamnatin kasar Amurka ta nuna damuwarta kan irin kisan kiyashin da ake yiwa yan Arewacin Najeriya.

Gwamnatin Amurka a jawabin da sakataren harkokin wajenta, Mike Pompeo, ya ce wannan kashe-kashe ya zama rashin hankali.

Amurkan ta yi kira ga Buhari ya dau matakai don tabbatar da cewa ya magance matsalar tsaro a kasar,

A ranar Lahadi, Premium Times ta yi kididdiga kuma ta gano cewa an hallaka bayin allah 140 cikin yan kwanakin nan kuma bila adadin sun jikkata.Saurari karashen labarin..

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel