Sakon Sultan ga Buhari: Ƴan Najeriya na da ikon yin zanga-zanga kan tsaro

Sakon Sultan ga Buhari: Ƴan Najeriya na da ikon yin zanga-zanga kan tsaro

Shugaban Jama’atu Nasril Islam, JNI, Sultan Muhammed Sa’ad Abubakar III ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya dauki matakin kawo karshen rashin tsaro a kasar ko da kuwa makiyansa na da hannu ciki.

Wannan kirar ta Sultan na dauke ne cikin wata sanarwar da sakataren JNI, Dr Khalid Abubakar Aliyu ya fitar mai taken ‘Kallubalen tsaron Najeriya: A dauki mataki ba wai tir da hare-haren ba’.

A cewar Sarkin Musulmin, Yan Najeriya suna da ikon su bayyana ra'ayoyinsu a kan kashe-kashen da ake yi a kasar musamman a yankin arewa kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

'Yan Najeriya na da ikon yin zanga-zanga a kan kashe-kashe: Sultan ga Buhari
'Yan Najeriya na da ikon yin zanga-zanga a kan kashe-kashe: Sultan ga Buhari. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Edo 2020: APC ta fitar da kwamitin zaben fidda gwani da na daukaka kara (Sunaye)

Wani sashi daga cikin sanarwar ya ce, "Kungiyar JNI, karkashin jagorancin mai alfarma, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, Sultan na Sokoto kuma shugaban JNI, ta gigita game da yawaitan rasa rayuka da dukiyoyi sakamakon harin yan bindiga, Boko Haram da masu fyade.

"Idan da gwamnati ta dauki matakan da suka dace domin magance matsalar da ba a sake samun afkuwar hare-haren ba.

"Duk da haka, munyi tir da wannan aikin zaluncin da halin jan kafa da hukumomin tsaro ke yi bayan kiraye kirayen mutane duk da cewa ayyuka sun musu yawa.

"Muna kira ga gwamnati ta saurari korafin mutane da shawarwarin da aka bayar ta kawo karshen wannan matsalar duk da cewa tana ikirarin akwai wasu da ke yi mata zagon kasa.

"Ya kamata gwamnati ta sani cewa yan kasa suna da ikon fadin ra'ayoyinsu a kan kallubalen rashin tsaro a Najeriya.

"Yawaitar asarar rayuka da dukiyoyi da ake yi a Borno, Katsina, Sokoto, Zamfara, Niger da wasu jihohi kaman Adamawa, Kaduna da Taraba lamari ne da ya kamata ya hana gwamnati barci.

"A halin yanzu, kamata ya yi a dauki matakin kawo karshen matsalar ba wai a rika maganar fatar baki ba kawai na yin Allah wadai da hare-haren."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel