Dakarun soji sun halaka 'yan Boko Haram 25, sun ceto mutum 33

Dakarun soji sun halaka 'yan Boko Haram 25, sun ceto mutum 33

Rundunar Operation Lafiya Dole ta tabbatar da halaka mayakan Boko Haram 25 tare da ceto mutum 33 da suka yi garkuwa da su.

Shugaban fannin yada labarai na tsaro, Manjo Janar John Enenche, ya ce rundunar soji da ke sansani na 11 a Gamboru da ke karamar hukumar Ngala ta jihar Borno ne suka yi namijin kokarin.

Lamarin ya faru a ranar 14 ga watan Yunin 2020 bayan dakarun sun isa kauyen Kusumu da Warshele, yankin da aka tabbatar 'yan ta'addan na boye makamai.

Ya ce dakarun sojin sun kara da duba Kumo, Diime da Sabori inda suka yi musayar ruwan wuta da wasu mayakan Boko haram da ke buya a yankin.

"Bayan arangamar da suka yi, dakarun sun kashe mayakan Boko Haram 13 tare da kwace bindigogi 21, abubuwa masu fashewa, tutocin Boko Haram 2, adduna 5, digga daya, mashi daya, kekuna biyar, babura 3, amalanke 5, amsa kuwwa biyu da janareto daya.

"Dakarun sun kara da ceto mutum 32 da mayakan ta'addancin suka yi garkuwa da su. 16 daga ckinsu mata ne yayin da 16 suka kasance kananan yara," yace.

Dakarun soji sun halaka 'yan Boko Haram 25, sun ceto mutum 33
Dakarun soji sun halaka 'yan Boko Haram 25, sun ceto mutum 33. Hoto daga Leadership
Asali: Twitter

KU KARANTA: Harbi a Aso Rock: An sauyawa masu tsaron Aisha Buhari wurin aiki

Har ila yau, dakarun sun kai samame yankin Pulka da ke karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno a ranar 11 ga watan Yunin 2020 inda suka fatattaki 'yan ta'addan da ke Pulka zuwa Bokko da Kirawa.

Dakarun sun ci karo da wasu mayakan ta'addancin inda suke kokarin tsallaka tsaunikan Mandara da Banki tare da wasu kayayyakin amfani.

A take suka halaka biyu daga ciki sannan wasu suka tsere da raunikan harbin bindiga, jaridar Leadership ta wallafa.

Har ila yau, kwamandan Boko Haram, Abu Imrana ya rasa ransa sakamakon musayar wutar da ta shiga tsakanin mayakan ta'addancin da dakarun sojin Najeriya a jihar Borno.

Wata majiya daga jami'an tsaro ta bayyana hakan ga jaridar The Cable a ranar Litinin. Ta ce Imrana na daga cikin manyan kwamandojin da dakarun suka halaka, lamarin da ya girgiza 'yan ta'addan don yana daga cikin shugabanni masu rinjaye.

Boko Haram ta sabunta hare-harenta ga dakarun sojin Najeriya da ke yankin arewa maso gabas a cikin kwanakin nan.

A kalla mutum 150 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren 'yan ta'addan Boko Haram a kananan hukumomin Monguno da Gubio na jihar Borno a makon da ya gabata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel