Ma'aikatan lafiya 29 sun kamu da COVID-19 a Plateau

Ma'aikatan lafiya 29 sun kamu da COVID-19 a Plateau

Gwamnatin Jihar Plateau a ranar laraba ta bayyana cewa ma'aikatan lafiyanta ashirin da tara (29) sun kamu da wannan cutar mai toshe numfashi watau Coronavirus

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar, Dr Nimkong Lar, ne ya bayyana haka yayin da yake hira da manema labarai a garin Jos.

A cewarshi, mutum 198 suka kamu da cutar, an sallami mutum 114 yayinda 5 suka riga mu gidan gaskiya.

"Alkaluman cibiyar takaita yaduwar cututtuka na kasa ya nuna cewa mutum 168 ne suka kamu da cutar a jihar amma yanzu sakamakon da aka saki ya nuna cewa mutum 198 ne suka kamu," Inji shi.

Ma'aikatan lafiya 29 sun kamu da COVID-19 a Plateau
Ma'aikatan lafiya 29 sun kamu da COVID-19 a Plateau
Asali: UGC

KU KARANTA: Shugaba Muhammadu Buhari ya shiga ganawar sirri da hafsoshin tsaro

Dr. Lar yace jihar ta rufe wani asibiti mai zaman kanshi na tsawon makonni biyu, bayan an samu bullar cutar a jikin mutum biyu wadanda ake kula da su saboda wasu cutuka daban.

Ya kara da cewa an samu kwayar cutar a jikin 17 daga cikin ma'aikatan asibitin, yayinda aka killace dukkan ma'aikatan asibitin.

"Mun yiwa asibitin feshi jiya sannan mun rufe shi saboda lafiyar jama'a.

"Mun kuma dauki ma'aikatan 17 zuwa cibiyar killacewa domin a kula dasu," Inji shi.

A wani bangaren, gwamnatin jihar ta koka da yadda mutane da kungiyoyi basa bin dokokin da aka shimfida domin takaita yaduwar cutar bayan da gwamnan jihar, Simon Lalong ya sassauta dokar kulle a ranar 11 ga watan Yuni.

A wani labarin daban, Kungiyar Likitocin Najeriya ta siffanta barazanar gwamnatin tarayya na sallamarsu daga aiki ko kin biyansu albashi idan basu koma bakin aiki ba a matsayin wasan yara.

Shugaban kungiyar, Aliyu Sokomba, ya bayyana cewa "barkwanci kawai gwamnati keyi" kuma ko kadan hakan ba zai baiwa Likitoci tsoro ba.

Hakazalika ya lashi takobin cewa za su cigaba da yajin aikinsu har sai an biyasu dukkan bukatunsu.

A ranar Talata, gwamnatin tarayya ta yi barazanar sallamar likitocinta daga aiki muddin ba su yi watsi da maganar zuwa yajin-aiki, su ka koma asibitoci domin su cigaba da kula da marasa lafiya ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel