Yadda za a shawo kan matsalar 'yan bindiga a Katsina - Shugaban manoma

Yadda za a shawo kan matsalar 'yan bindiga a Katsina - Shugaban manoma

Shugaban kungiyar manoma ta Najeriya (AFAN), Kabir Ibrahim, ya ce dole ne a dauka mataki mai tsauri a dukkan dazuzzukan kasar nan don samar da tsaro ga mutane game da 'yan bindiga, masu satar Shanu.

Shugaban manoman wanda dan asalin karamar hukumar Faskari ne, cibiyar rikicin 'yan bindigar jihar Katsina, ya ce babbar hanyar maganin 'yan bindigar shine markade wasu sassa na dajin, al'amarin da yace masu rajin kare sauyin yanayi za su soka.

A tattaunawar Ibrahim da Daily Trust, ya ce dazuzzukan ne suka zama maboyar 'yan bindigar saboda a cushe suke kuma ba a iya shiga. Ya ce manoma basu iya zuwa gonakinsu wanda yace zai iya kawo yunwa nan gaba kadan.

Ibrahim ya ce duk da gwamnati na iyakar kokarinta wajen dakile ayyukan miyagun, akwai takaici a ce mutane su fara tantamar gazawar jami'an tsaro sai kace sun fi su iya yakar ta'addanci.

Ya ce yana da tabbacin cewa 'yan bindigar sun san duk wani aiki na jami'an tsaron saboda akwai masu kai musu bayanai a dukkan kananan hukumomi da abun ya shafa.

Yadda za a shawo kan matsalar 'yan bindiga a Katsina - Shugaban manoma
Yadda za a shawo kan matsalar 'yan bindiga a Katsina - Shugaban manoma. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ba zan iya da jarabarsa ba, tsawon dare babu sassauci - Matar aure mai neman saki

A don haka yace, "Jami'an tsaro su gujewa bayyana ayyukansu saboda hakan na bada gudumawa wurin rashin nasararsu.

"Yan bindiga suna da wayon gaske kuma suna kai hari ne a wuraren da jami'an tsaro suka bari babu dadewa."

Ya kara kira ga dukkan jami'an tsaro da ke da alhakin kare rayukan jama'a da su dage wurin sauke nauyinsu.

"A bar 'yan sa kai su yi wa sojoji jagora zuwa maboyar 'yan bindigar da dukkan mutanen da ake zargi na da sa hannu a aika-aikar," yace.

Har ila yau, hedkwatar tsaro ta kasa ta ce rundunar Operation Hadarin Daji ta ragargaza sansanin 'yan bindiga tare da halaka wasu har lahira a dajin Katsina da ke kudancin Birnin Kogo kusa da iyakar Katsina da Zamfara.

Shugaban fannin yada labarai na rundunar sojin Najeriya, John Enenche, a wata takarda da ya fitar a Abuja, ya ce samamen da suka kai ci gaba ne na kawo karshen ta'addanci a yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya a kasar nan.

Enenche ya ce an aiwatar da harin ta jiragen yaki ne a ranar Litinin karkashin wani sashi na atisayen Operation Accord bayan bayanan sirri da dakarun suka samu na maboyar 'yan ta'addan.

Ya yi bayanin cewa, bayanan sun nuna tabbaci a kan maboyar 'yan bindigar na nan inda wasu bukkoki suke.

Suna amfani da wurin a matsayin karamin sansani wanda shahararren dan bindiga "Adamu Aleiro" ke jagoranta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel