COVID-19: An kwantar da shugaban kasar Honduras a asibiti

COVID-19: An kwantar da shugaban kasar Honduras a asibiti

An kwantar da Shugaba Juan Orlando Hernandez na kasar Honduras a asibiti a babban birnin kasar ta Tegucigalpa bayan an sanar da cewa ya kamu da coronavirus a ranar Laraba.

Likitocin da suka duba shugaban kasar sun ce sakamakon binciken da aka yi masa ya nuna yana fama da ciwon pneumonia kamar yadda kakakin gwamnati, Francis Contreras ya shaidawa manema labarai.

COVID-19: An kwantar da shugaban kasar Honduras a asibiti
COVID-19: An kwantar da shugaban kasar Honduras a asibiti. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

Ya kara da cewa, "akwai wasu kwayoyin cuta da suka shiga huhun Hernandez amma yana cikin koshin lafiya."

DUBA WANNAN: Edo 2020: Akwai yiwuwar Obaseki ya koma APC - Kakakinsa

Shugaban kasar mai shekara 51 a ranar Talata ya sanar da cewa baya jin dadin jikinsa kuma a karshen mako aka gano cewa kwayar cutar COVID-19 ce.

Sanarwar da gwamnatin ta fitar ya ce, "Hernandez yana kiyaye dukkan matakan kare kansa daga cutar da hukumomin lafiya suka bayar amma saboda yanayin aikinsa yana da wahala dena cudanya da mutane."

Matarsa, Ana Garcia ita ma ta kamu da kwayar cutar ta coronavirus amma a halin yanzu ba ta da alamomin cutar a cewar jamian gwamnatin kasar.

Honduras na cikin kasashen duniya da annobar ta coronavirus ta yi wa illa sosai inda mutane da yawa a biranen Tegucigalpa da San Pedro Sula suka kamu da cutar.

Kawo yanzu fiye da mutum 9,000 sun kamu da cutar a kasar yayinda mutum 322 sun mutu.

Kwararru sun yi ikirarin cewa adadin wadanda suka kamu da cutar a kasar ya dara 9,000 duba da cewa mutum 1,000 kawai ake yi wa gwaji a kowacce rana.

A wani labarin na daban wasu yara biyu da ba a ambaci sunansu ba sun rasa rayyukansu a ranar Laraba bayan gini ya rufta a kansu a Gafari Balogun na Ogudu da ke jihar Legas.

Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa na jihar Legas, Olufemi Oke-Osanyintolu ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Ya ce ginin ya rufta ne sakamakon ruwan sama mai karfi. Ya kara da cewa wadanda suka mutu kananan yara ne kuma an ciro gawarwakinsu daga baraguzan ginin.

"An kira LASEMA misalin karfe 12.40 na rana a kan wani gini mai hawa daya da ya rufta a Gafari Balogun Streer da ke Ogudu.

"Da isarsu wurin da abin ya faru, jamian hukumar sun lura cewa ginin ya rufta ne sakamakon cin ruwa a kasar ginin.

"An sanar da su cewa ginin ya rufta wa yara biyu, daya na miji, dayan kuma mace. Nan take suka bazama aikin ceto yaran amma ko da suka gano su yaran biyu sun riga sun mutu.

"An tafi da gawarsu zuwa asibiti don ajiye su a dakin ajiyar gawa. Za a gudanar da gwajin inganci a sauran ginin da ya bai rufta ba da a yanzu an rufe wurin," in ji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel