Me kika taba yi don inganta rayuwar yara- 'Yan Najeriya sun caccaki Aisha Buhari

Me kika taba yi don inganta rayuwar yara- 'Yan Najeriya sun caccaki Aisha Buhari

Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sha caccaka tare da suka a kafar sada zumuntar zamani bayan ta yi wallafar tunawa da ranar yaran Africa.

A ranar Talata, uwargidan shugaban kasar ta je shafinta na Twitter inda ta saka bidiyon yaran Najeriya sun tattaunawa a kan cin zarafi, rikici da fyade.

Ta yi kira ga 'yan Najeriya da su tallafa wurin samar da damar da yara zasu yi amfani da baiwarsu yadda ya dace.

"A yayin da muke tunawa da ranar yara ta duniya, muna son su zamo wani bangare namu ta yadda za su zama masu amfani a gaba," ta rubuta.

A take wannan wallafar ta janyo cece-kuce daga ma'abota amfani da kafar. Tuni suka nuna rashin gamsuwarsu ta hanyar yi mata tsokaci masu zafi.

"Ki yi wani abu a kan almajirai da ke yawo a titunan Arewacin Najeriya," wani mai amfani da Twitter yace.

"Haba uwargidan shugaban kasa, me kika yi a kan gina rayuwar yaran Afrika? Ta yaya kike so su zama shugabannin gobe? Fada mana abinda kike yi ba wanda kike son yi ba," wani yayi martani.

KU KARANTA: Ba zan iya da jarabarsa ba, tsawon dare babu sassauci - Matar aure mai neman saki

Wani ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani na Twitter kuwa cewa yayi, "Wannan magana akwai dadin ji. Amma ki sanar da maigidanki cewa a yadda yake tafiyar da kasar nan, da wuya yaran su zama manyan gobe.

"Yaran na mutuwa sakamakon ayyukan 'yan bindiga da rashin cibiyoyin kiwon lafiya masu kyau."

Me kika taba yi don inganta rayuwar yara- 'Yan Najeriya sun caccaki Aisha Buhari
Me kika taba yi don inganta rayuwar yara- 'Yan Najeriya sun caccaki Aisha Buhari. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

Hakazalika, dukkan jami'an tsaron da ke da hannu a harbin da aka yi a fadar shugaban kasa da ke Abuja an sako su kuma an sauya musu wurin aiki.

Majiya mai karfi ta sanar da Daily Trust a daren jiya cewa, wadanda aka sauya wa wurin aikin duk hadiman Aisha Buhari ne har da ADC dinta, Usman Shugaba tare da kwamandan dogaranta.

A daya bangaren kuwa, mataimaki na musamman ga shugaban kasa, Sabiu Tunde Yusuf, ya koma bakin aikinsa inda yayi watsi da bukatar killace kansa bayan dawowa daga Legas.

Sabiu, wanda aka fi sani da Tunde, sunan da ya samu daga Tunde Idiagbon, an ganshi a fadar shugaban kasar da ke Abuja a jiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: