Katsina: An umurci shugaban Jami'ar Dutsin-Ma ya sauka daga mukaminsa

Katsina: An umurci shugaban Jami'ar Dutsin-Ma ya sauka daga mukaminsa

Kotun Da'ar Ma'aikata ta Kasa da ke Abuja a jiya ta umurci Farfesa Armaya'u Hamisu Bichi ya yi biyaya ga umurnin da ta bayar a baya ya dena gabatar da kansa a matsayin shugaban Jami'ar Tarayya ta Dutsimna a Katsina.

Da aka fara sauraron karar mai lamba NICN/ABJ/87/2020 da Farfesa Haruna Abdu Kaita ya shigar, lauyan shugaban jamiar da aka dakatar, Barrister Abdulsalam Saleh ya shaidawa kotu cewa umurnin kotu ba ta isa hannunsa ba.

Amma, Mai shari'a Oyebiola Oyewumi da ke sauraron karar ya umurci a sake mika wa Barrister Saleh umurnin na kotu nan take inda ya karba a madadin wanda ya ke kare wa.

Katsina: An umurci shugaban Jami'an Dutsin-Ma ya sauka daga mukaminsa
Katsina: An umurci shugaban Jami'an Dutsin-Ma ya sauka daga mukaminsa. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Edo 2020: Akwai yiwuwar Obaseki ya koma APC - Kakakinsa

A baya, Barrister Saleh ya shaidawa kotu cewa Ma'aiktar Ilimi ta Tarayya ta aika wa Farfesa Bichi takarda a kan karar da aka shigar game da nadinsa.

Kafin cigaba da sauraron shari'ar a ranar 7 ga watan Yulin 2020, Mai sharia Oyewumi ya umurci lauyan Farfesa Bichi ya kammala shirye hujjojinsa a kan lokaci.

Da aka tuntube shi don ji ta bakinsa a kan hukuncin kotun, Farfesa Bichi ya ce tunda lamarin na gaban kotu ba zai yi tsokaci a kai ba kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A wani labarin daban Gwamnatin tarayyar Najeriya ta saki fursunoni 6,590 da ke tsare a gidajen gyaran hali daban daban a sassar kasar.

Hakan na kunshe ne cikin wani rubutu da Attoney Janar na kasa, AGF, kuma ministan Shari'a, Abubakar Malami, SAN, ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Laraba 17 ga watan Yuni.

A cewar Malami, fursunonin sun cika ka'idojin da aka gindaya na sakin fursunoni daga gidajen gyaran hali 32.

Ministan yayin da ya ke gabatar da nasarorin da ma'aikatarsa ta samu daga 2015 zuwa 2020 ya ce ya taka muhimmiyar rawa wurin ganin an rage cinkoso a gidajen gyaran hali a wasu jihohi 14.

Idan za a iya tunawa, Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci a bullo da hanyoyin gaggauta sharia da rage cinkosu a gidajen gyaran hali a kasar sakamakon bullar annobar coronavirus.

Fadar shugaban kasar ta bakin mashawarcin shugaban kasa na musamman kan kafafen watsa labarai, Femi Adesina ne ya bayyana hakan a ranar Laraba 22 ga watan Afrilu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel