Maƙiya a gwamnatin Buhari ke neman ganin bayan arewa - Sarkin Katsina

Maƙiya a gwamnatin Buhari ke neman ganin bayan arewa - Sarkin Katsina

Mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya ce ya sha fada wa Shugaba Muhammadu ya rika kula da makiya da ke ciki da wajen gwamnatinsa.

Sarkin ya yi ikirarin cewa wadannan makiyan ne suke kokarin tarwatsa yankin arewa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya yi wannan jawabin ne a ranar Laraba yayin da ya ke magana da tawagar gwamnatin tarayya karkashin jagorancin mai bawa shugaban kasa shawara a kan tsaro, Janar Babagana Monguna (mai ritaya).

Maƙiya a gwamnatin Buhari ke neman ganin bayan arewa - Sarkin Katsina
Maƙiya a gwamnatin Buhari ke neman ganin bayan arewa - Sarkin Katsina. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

Tawagar da ta hada da Sufeta Janar na Yan sanda, Mohammed Adamu, Shugaban DSS, Yusuf Magaji Bichi da Direktan Hukumar NIA, Ahmed Rufai sun ziyarci Katsina ne don yin jaje bisa kisar da yan bindiga suka yi a baya bayan nan.

DUBA WANNAN: Edo 2020: Akwai yiwuwar Obaseki ya koma APC - Kakakinsa

Tawagar ta kuma ziyarci jihar ne domin tabbatar musu da cewa gwamnati na iya kokarin ta wurin ganin ta magance kallubalen tsaro a jihar da wasu yankunan kasar.

Idan za a iya tunawa, Kakakin Shugaba Buhari, Garba Shehu a hirar da aka yi da shi a Channels Television a ranar Litinin ya yi ikirarin cewa wasu masu sarautar gargajiya a Katsina na taimakawa yan bindiga.

Ya ce wasu masu sarautan da bai ambaci sunan su ba suna taimakawa yan bindigan su tsere duk lokacin da jamian tsaro ke shirin kai musu hari.

Sai dai wasu mazauna Katsina daga bisani sun kallubalanci fadar shugaban kasar ta bayyana sunayen masu sarautar gargajiyan ta yi ikirarin suna taimakawa yan bindiga a jihar.

Sarkin na Katsina tare da Sarkin Daura, Umar Faruk da wasu masu sarautan gargajiya a jihar da suka tarbi tawagar gwamnatin a jiya Laraba sun ce sun gode da ziyarar.

Sarkin ya ce,"Na sha fada wa shugaban kasa ya kula da makiya da ke ciki da wajen gwamnatinsa. Suna son tawartsa gwamnatinsa da arewa. Idan ka lalata Buhari, ka lalata arewa da Najeriya."

Tawagar a jiya Laraba ta kai irin wannan ziyarci jihar Sokoto.

Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar yayin tarbarsu a fadar sa ya ce akwai bukatar gwamnati ta kara dage wa domin kawo karshen wannan kashe kashen.

Sai dai ya ce ziyarar da tawagar shugaban kasar ta kai ya nuna cewa shugaban bai manta da yankin arewa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel