Garkame shugaban matasan Arewa zai iya janyo tashin hankalin da ba a zato - Bashir Tofa ya gargadi Buhari

Garkame shugaban matasan Arewa zai iya janyo tashin hankalin da ba a zato - Bashir Tofa ya gargadi Buhari

Tsohon dan takarar kujeran shugaban kasa, kuma shugaban kungiyar dattawan jihar Kano, Alhaji Bashir Tofa, ya ce kama Nastura Sharrif, shugaban gamayyar kungiyoyin Arewa ya sabawa demokradiyya.

A jawabin da ya saki, Alhaji Tofa ya ce damke matashin na nuna rashin son jin gaskiya kuma ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin sakeshi da gaggawa.

Ya ce idan ba'a sakeshi ba za a iya tayar da wani sabon rikicin da kashe wutar zai yi matukar wuya.

Garkame shugaban matasan Arewa zai iya janyo tashin hankalin ba a zato - Bashir Tofa ya gargadi Buhari
Bashir Tofa ya gargadi Buhari
Asali: UGC

Tofa yace: "Damke Alhaji Nasturah Ashir Sharrfi, shugaban matasan Arewa bai dace ba, ya sabawa demokradiyya kuma yana nuna rashin son jin gaskiya. Babu hankali ciki kuma babu adalci."

"Ko lokacin mulkin kama karya, mutane na iya zanga-zanga kan lamuran da suka shafi al'umma kuma ba za'a kamasu ba. Shin ana nuna mana cewa mutum ba zai iya bayyana ra'ayinsa cikin lumana ba?

"Shin wannan demokradiyya ne da Najeriya ke kokarin nunawa duniya?

"Ina kira ga shugaban kasa ya bada umurnin sakin wannan matashin da gaggawa kuma a bashi hakuri kafin a tayar da kurar da ba za a iya kwantarwa ba idan ta game Arewa da Najeriya ma gaba daya."

"Mutane na matukar fushi kan yadda abubuwa da dama ke gudana. Idan kuma aka tsakuri mutane a inda ke musu ciwo, kuma wasu yan tsiraru suka tunzura wasu marasa ji, abubuwa ba zasuyi kyau ba."

"Rikicin zaben 2011 inda akayi asarar rayuka da dukiyoyi saboda jita-jitan cewa an hana Janar Muhammadu Buhari mulki zai zam tamkar somin tabi idan rikici ya barke yanzu."

"Yan Najeriya na cikin bacin rai! Matsalar tsaro ko ina, talauci, rashin aiki, yanzu kuma COVID-19, duk sun karar da hakurin mutane."

"Shugaba Buhari ya yi hattara. Ya kamata ya fara sanin ainihin abokansa na gaskiya da makiyansa, wadanda ke bata sunansa da rana gobensa."

"Ya kamata ya tuna cewa nan da shekara uku, wani ne zai zama shugaban kasa."

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa Bayan zanga-zangar lumanar da matasa suka yi sakamakon rashin tsaro da yayi kamari a jihar, jami’an ‘yan sanda sun kama shugaban gamayyar kungiyoyin matasan Arewa watau Coalition of Northern Groups (CNG), Nastura Ashir Sharif.

A wata takardar da kakakin kungiyar, Abdulazeez Suleiman yasa hannu, yace an kama Sharif bayan sun kammala zanga-zangar da suka yi a Katsina a ranar Talata.

Idan zamu tuna, a ranar Talata, dubban matasa daga jihohin arewa karkashin inuwar CNG suka hadu a Katsina inda suka yi zanga-zanga a kan ta'azzar ayyukan ‘yan bindiga a yankin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel