Da dumi-dumi: Bayan mutuwar Sanata mai cutar Korona, an garkame majalisar dokokin tarayya

Da dumi-dumi: Bayan mutuwar Sanata mai cutar Korona, an garkame majalisar dokokin tarayya

An garkame majalisar dokokin tarayya dake kwaryar birnin tarayya Abuja domin feshi saboda tsoron cutar annobar Coronavirus da ta hallaka mutane 469 a Najeriya.

Takarda da aka saki mai lamba NASS/HR/MSD/ClR/003/IV138 a ranar 17 ga Yuni, 2020, ya bayyana cewa za'a kulle majalisar na tsawon kwanaki biyu.

Takardar da mataimakin dirakta, Titus Jatau, ya rattaba hannu yace: "An bada umurni yin feshi daga gobe Alhamis, 18 da Juma'a 19, ga Yuni, 2020.

"Saboda haka, muna kira ga dukkan ma'aikata su nisanta daga majalisa wannan lokacin kuma kada su dawo aiki sai ranar Litinin, 22 ga Yuni, 2020."

Da dumi-dumi: Bayan mutuwar Sanata mai cutar Korona, an garkame majalisar dokokin tarayya
Da dumi-dumi: Bayan mutuwar Sanata mai cutar Korona, an garkame majalisar dokokin tarayya
Asali: Depositphotos

Wannan rufe majalisa ya tayar zarge-zargen alamun yaduwar cutar Korona a majalisar dokokin.

Za ku tuna cewa gwamnatin jihar Legas ta bayyana cewa Sanatan ya mutu kwanaki biyu da suka gabata, Sikiru Adebayo Osinowo, ya mutu ne sakamakon cutar Coronavirus.

Dan majalisan wanda ya wakilci yankin Legas ta gabas ya rasu ne a babbar asibitin First Cardiologist Hospital, dake Legas.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel