FG ta rage cinkoso a gidajen gyaran hali, ta saki fursunoni 6,590

FG ta rage cinkoso a gidajen gyaran hali, ta saki fursunoni 6,590

- Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sako fursunoni 6,590 daga gidajen gyaran hali daban-daban a fadin kasar

- Abubakar Malami, Ministan Sharia kuma Attoney Janar na kasar ne ya sanar da hakan a ranar Laraba 17 ga watan Yuni

- Ministan ya ce an sako fursunonin ne sakamakon yunkurin da gwamnati ke yi don rage cinkoso a gidajen gyaran halin

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta saki fursunoni 6,590 da ke tsare a gidajen gyaran hali daban daban a sassar kasar.

Hakan na kunshe ne cikin wani rubutu da Attoney Janar na kasa, AGF, kuma ministan Shari'a, Abubakar Malami, SAN, ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Laraba 17 ga watan Yuni.

A cewar Malami, fursunonin sun cika ka'idojin da aka gindaya na sakin fursunoni daga gidajen gyaran hali 32.

FG ta rage cinkoso a gidajen gyaran hali, ta saki fursunoni 6,590
FG ta rage cinkoso a gidajen gyaran hali, ta saki fursunoni 6,590
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Edo 2020: APC ta fitar da kwamitin zaben fidda gwani da na daukaka kara (Sunaye)

Ministan yayin da ya ke gabatar da nasarorin da ma'aikatarsa ta samu daga 2015 zuwa 2020 ya ce ya taka muhimmiyar rawa wurin ganin an rage cinkoso a gidajen gyaran hali a wasu jihohi 14.

Idan za a iya tunawa, Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci a bullo da hanyoyin gaggauta sharia da rage cinkosu a gidajen gyaran hali a kasar sakamakon bullar annobar coronavirus.

Fadar shugaban kasar ta bakin mashawarcin shugaban kasa na musamman kan kafafen watsa labarai, Femi Adesina ne ya bayyana hakan a ranar Laraba 22 ga watan Afrilu.

Shugaban na Najeriya a wasikar da ya aike wa Alkalin Alkalan Najeriya, Tanko Muhammad ya tunatar da shi rokon da Majalisar Dinkin Duniya ta yi ga kasashe su rage cinkoso a gidajen gyran hali na kasashensu don samar da tazara.

A wani labarin, kun ji cewa wasu kananan yara biyu da ba a ambaci sunansu ba sun rasa rayyukansu a ranar Laraba bayan gini ya rufta a kansu a Gafari Balogun na Ogudu da ke jihar Legas.

Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa na jihar Legas, Olufemi Oke-Osanyintolu ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Ya ce ginin ya rufta ne sakamakon ruwan sama mai karfi.

Ya kara da cewa wadanda suka mutu kananan yara ne kuma an ciro gawarwakinsu daga baraguzan ginin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel