Yadda gini ya rufto ya kashe yara biyu a Legas

Yadda gini ya rufto ya kashe yara biyu a Legas

Wasu kananan yara biyu da ba a ambaci sunansu ba sun rasa rayyukansu a ranar Laraba bayan gini ya rufta a kansu a Gafari Balogun na Ogudu da ke jihar Legas.

Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa na jihar Legas, Olufemi Oke-Osanyintolu ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Ya ce ginin ya rufta ne sakamakon ruwan sama mai karfi.

Ya kara da cewa wadanda suka mutu kananan yara ne kuma an ciro gawarwakinsu daga baraguzan ginin.

Yadda gini ya rufto ya kashe yara biyu a Legas
Yadda gini ya rufto ya kashe yara biyu a Legas. Hoto daga LIB
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Buhari ya nada sabbin sakatarorin dindindin 12 (Sunaye da jihohi)

"An kira LASEMA misalin karfe 12.40 na rana a kan wani gini mai hawa daya da ya rufta a Gafari Balogun Streer da ke Ogudu.

"Da isarsu wurin da abin ya faru, jamian hukumar sun lura cewa ginin ya rufta ne sakamakon cin ruwa a kasar ginin.

"An sanar da su cewa ginin ya rufta wa yara biyu, daya na miji, dayan kuma mace. Nan take suka bazama aikin ceto yaran amma ko da suka gano su yaran biyu sun riga sun mutu.

"An tafi da gawarsu zuwa asibiti don ajiye su a dakin ajiyar gawa.

"Za a gudanar da gwajin inganci a sauran ginin da ya bai rufta ba da a yanzu an rufe wurin," in ji shi.

A wani labari na daban, wasu dalibai a kwallejin fasaha da ke Nekede a garin Owerri na jihar Imo sun mutu yayin gasar yin lalata.

Daliban, Cynthia Obieshi da Samuel Osuji sun mutu ne a ranar Lahadi kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Mai magana da yawun rundunar yan sanda ta jihar, Orlando Okeokwu ya ce an kai gawarwakin daliban asibiti don ajiye wa a dakin adana gawarwaki.

Ya ce, "A ranar Lahadi, 14 ga watan Yuni ta 2020 bayan samun rahoto jami'an 'yan sanda da ke Hedkwatan Rundunar da ke Nekede/Ihiagwa, sun tafi daki mai lamba 19, a Vic-Mic Lodge da ke JMJ Bus stop.

"Sun kutsa cikin dakin inda suka tsinci gawarwakin wata Cynthia Obieshi da Samuel Osuji.

"An gano cewa ita Cynthia ta ziyarci saurayinta, Samuel a ranar 13 ga watan Yunin 2020 inda ta kwana tare da shi amma da gari ya waye dukkansu ba su farka ba.

"Binciken da kwararru suka fara gudanarwa ya nuna akwai yiwuwar sun mutu ne sakamakon kwayoyi da suka sha.

"A halin yanzu dai an kai gawarwarkinsu dakin ajiyar gawa yayin da ake cigaba da gudanar da bincike a kan lamarin."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel