Yanzu-yanzu: Najeriya ta yi asarar bilyan 17 cikin watanni 5 sakamakon barayin mai - NNPC

Yanzu-yanzu: Najeriya ta yi asarar bilyan 17 cikin watanni 5 sakamakon barayin mai - NNPC

Babban kamfanin man feturin Najeriya NNPC ya bayyana cewa cikin watanni biyar da rabi da suka gabata na shekarar nan, kasar nan ta yi asarar $48 million (N17 billion) sakamakon barayin man fetur.

Dirakta Manajan NNPC, Mallam Mele Kyari, ya bayyana hakan a zama da kwamitin sashen man fetur na majalisar dattawan tarayya.

Amma ya kara da cewa asarar da akayi wannan shekarar ba kai wanda akayi a shekarun baya ba.

A 2018, an yi asarar $825 million (N297 Billion) yayinda a 2019 akayi asarar $725 million (N261 Billion).

Ya ce an samu ragi ne saboda inganta lura da jami'an tsaro sukayi.

Ya ce tare da hadin baki wasu jami'an tsaro, mutanen gari da shugabanninsu, ana fasa bututun man gwamnati don sata.

KU KARANTA: Bayan kashe-kashe da zanga-zanga, IGP, NSA, da shugaban DSS, shugaba NIA sun dira Katsina

Yanzu-yanzu: Najeriya ta yi asarar bilyan 17 cikin watanni 5 sakamakon barayin mai - NNPC
Mele Kyari - Shugaban NNPC
Asali: UGC

A cewarsa, yanzu sun yanke shawara mayar da hakkin lura da bututun mai hannun jami'an tsaron sabanin yan kwagilan tsaro da aka saba baiwa.

Kan lamarin matatun man gwamnatin kuwa, Kyari ya ce da gan-gan NNPC ta rufe matatun man Kaduna, Warri da Fatakwal.

Yace: "Mun rufe matatun mai uku ne saboda dalilai guda biyu."

"Na farko mun yanke shawara ne saboda babu riba. Akwai sharadin kashi 70 zuwa 80 na arzikin danyen mai."

"Babu amfanin tace mai idan za'ayi asarar kashi 20 na arzikin danyen mai."

"Na biyu shine babu tabbacin samun isasshen danyen man da zamu tura matatun nan."

A bangare guda, A ranar Juma’a ne kamfanin man Najeriya na NNPC ya fitar da rahoton diddikin kudin da aka kashe.

Wannan ne karon farko da aka yi wannan a cikin shekaru 43 da kafuwar kamfanin.

Rahoton da aka fitar ya tike ne da karshen Dismaban 2018, inda ya nuna yadda sauran kamfanoni 20 da ke karkashin NNPC su ke gudanar da aikace-aikacensu a cikin gida da wajen Najeriya.

Kamfanonin da aka bayyana abin da su ke samu da abin da su ka kashe sun hada da kamfanonin tatar mai na NPDC, WRPC, PHRC, KRPC da ke garuruwan Fatakwal, Warri, da kuma Kaduna.

Sauran kamfanonin sun hada da IDSL, NPMC da NPSC masu saida kayan mai da kuma adana mai a bututun kasa. Har ila yau akwai kamfanoni irinsu NETCO, NGMC, UK, NAPIMS, da NIDAS.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel