APC tayi watsi da Giadom, ta tabbatar da shugabancin Ajimobi

APC tayi watsi da Giadom, ta tabbatar da shugabancin Ajimobi

Rikicin shugabanci da ake yi a jami'yyar All Progressives Congress, APC, mai mulki ya dauki sabon salo yayin da kwamitin zartarwa na jami'yyar ta sake jadada Abiola Ajimobi a matsayin shugaban riko.

Uwar jam'iyyar ta yi watsi da Victor Giadom, inda ta ce baya cikin 'yan kwamitin zartarwar tun lokacin da ya yi murabus domin ya yi takarar kujerar mataimakin gwamna a jihar Rivers.

Mataimakin shugaban jami'yyar ta APC na kasa shiyar Kudu maso Kudu, Hilliard Eta yayin jawabin da ya yi wa manema labarai bayan Giadom ya bar sakatariyar jam'iyyar ya ce an fara shirin zaben fidda gwani na gwamnan Edo.

APC tayi watsi da Gaidom, ta tabbatar da shugabancin Ajimobi
APC tayi watsi da Gaidom, ta tabbatar da shugabancin Ajimobi
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Buhari ya nada sabbin sakatarorin dindindin 12 (Sunaye da jihohi)

Kafin nadinsa Ajimobi ne mataimakin shugaban jamiyya na kasa na shiyar Kudu.

Jamiyyar ta jadada shugabancin Ajimobi ne yayin taron gaggawa karo na 45 da ta kira wanda ya samu hallarcin mutum 15 cikin mambobi 21 na NWC.

Hillary Eta wanda aka zaba domin jagorantar taron ya sanar da kafa kwamitin mutum bakwai da za su gudanar da zaben fid da gwani na gwaman jihar Edo da za ayi ranar 22 ga watan Yuni.

Gwamna Hope Uzodima na jihar Imo ne zai jagoranci kwamitin yayin da Sanata Ajibola Bashiru zai yi aiki a matsayin sakataren kwamitin.

Har wa yau, ya sanar da kafa wata kwamitin daukaka karar zabe na mutum biyar karkashin jagorancin Farfesa Mustapha Bello da Dr Kayode Ajulo a matsayin sakatare.

Eta ya jadada cewa Victor Giadom baya cikin NWC tun lokacin da ya yi murabus domin takarar mataimakin gwamna a Rivers a babban zaben da ta gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel