Dan kasuwan da ake zargi da satar N75m ya mutu yayin gwajin korona

Dan kasuwan da ake zargi da satar N75m ya mutu yayin gwajin korona

Wani dan kasuwa, Godwin Julius da ake bincika kan zargin damfara ta N75m ya mutu yayin da ake masa gwajin COVID-19 a Asibitin Cututtuka masu Yaduwa da ke Yaba a Legas.

An kama Godwin da wani Obinale Osunwoke ne a Ejigbo kuma an tsare su bayan 'yan sanda sun gano cewa kudaden da suke da shi mallakar wani hamshakin dan kasuwa ne da ya mutu.

Punch Metro ta ruwaito cewa 'yan sandan sun fara bincike a kansu ne yayin da wata kamfanin Amurka, Terraroad’s International Incorporation, Wisdom Chris, ta yi korafin cewa an mata damfara ta N75m.

Korona ta kashe dan kasuwa da ake zargi da damfara ta N75m
Korona ta kashe dan kasuwa da ake zargi da damfara ta N75m. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

Wisdom ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa wadanda ake zargin da yanzu suke tsare sunyi amfani da sunan Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola suka damfari kamfanin $200,000 da takardun bogi.

DUBA WANNAN: Tsohuwa mai shekara 65 ta auri ɗanta na riƙo mai shekara 24 (Hotuna)

"Kamfani na da ke Amurka ta yi karar wasu mutane da suka yi karya da sunan Ministan Ayyuka da Gidaje Babatunde Fashola.

"Sunyi kasuwanci da kamfani na kuma an damfari kamfanin kudi $200,000," in ji shi.

Ya kara da cewa, "Lokacin da muke son tabbatar da sahihancin takardun sai muka gano na bogi ne. Wadanda ake zargin daga bisani sun amsa cewa su yan damfara ne.

"Da farko mun dauki lauyoyi suyi bincike a kai amma da muka ga ba su bayar da hadin kai sai muka shigar da korafi wurin 'yan sanda."

Yayin binciken ne 'yan sanda suka samu izini daga kotu na kama Godwin da Osunwoke.

Sai dai Godwin ya fara rashin lafiya yayin da ake bincike kuma aka kai shi asibiti a Falomo inda likita ya bayar da shawarar a kai shi asibitin cututtuka masu yaduwa da ke Yaba don gwajin COVID-19.

Osunwoke ya yi ikirarin cewa 'yan sanda sun hana su zuwa kotu neman beli kuma lokacin da rashin lafiyar Godwin ta yi tsanani sun kai asibiti don gwajin COVID-19 inda ya mutu a nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel