Yanzun nan: Sakataren jam'iyyar APC ya dane kujerar shugaba, ya ce a sake tantance Obaseki

Yanzun nan: Sakataren jam'iyyar APC ya dane kujerar shugaba, ya ce a sake tantance Obaseki

Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa mataimakin sakataren na uwar jam'iyyar All Progressives Congress APC. Victor Giadom, ya kwace kujerar mukaddasshin shugaban jam'iyya.

Fara da iyawa, Victor Giadom ya sanar da cewa ya soke tantancewar yan takarar kujerar gwamnan jihar Edo da Adams Oshiomole ya gudanar, rahoton Channels TV.

Yayinda yake hira da manema labarai a hedkwatar jam'iyyar dake birnin tarayya Abuja ranar Laraba, Victor Giadom ya ce ya soke dukka abubuwan da kwamitin tantance yan takaran zaben Edo tayi.

Ya yi kira ga dukkan yan takaran su dawo yau (Laraba) da gobe (Alhamis) don sake sabon tantancewa.

A cewarsa, ba a yi adalci ba ace shugaban jam'iyyar da aka dakatar, Adams Oshiomole, ya jagoranci shirin tantance yan takarar zaben fidda gwanin duk da kasancewarsa abokin hamayyar gwamnan.

Ya ce ya yanke shawarar danewa kujerar ne bisa ga hukuncin babbar kotun tarayya na ranar 16 ga Maris inda aka dakatad da Oshiomole kuma aka umurcesa ya zama mukaddashi.

KU KARANTA: Bayan kashe-kashe da zanga-zanga, IGP, NSA, da shugaban DSS sun dira Katsina

Yanzun nan: Sakataren jam'iyyar APC ya dane kujerar shugaba, ya ce shi ya cancanta
Shugabanni uku kan kujera daya
Asali: Facebook

Yace: "Ina mai sanar muku da cewa a ranar 16 ga Maris 2020, Alkali S.U Bature a kara mai lambaFCT/HC/M/6447/2020 ya bada umurni bayan dakatad da Kwamred Adams Oshiomole cewa, Ni, Cif Victor Giadom, na zama mukaddashin shugaban jam'iyyarmu."

'Bamu samu damar aiwatar da umurnin ba saboda a ranar kuma kotun daukaka kara ta ce Oshimole ya cigaba da zama kan kujerarsa."

"Amma tun da jiya kotun daukaka karan ta cire damar da ta bashi kuma ba zamu iya barin kujerar babu kowa ba, ina mai sanar muku da cewa na dane kujerar mukaddashin shugaban uwar jam'iyyarmu bisa ga hukuncin kotu."

Da alamun akwai baraka cikin gidan jam'iyya yaryinda mutane uku ke ikiarin shugabanci bayan dakatad da Adams Oshiomole da kotu tayi.

Yayinda kwamitin gudanarwan jam'iyyar ta zabi surukin Ganduje, Abiola Ajimobi, mataimakin sakatare, Victor Giadom da mataimakin shugaba (Arewa), Lawal, na shelar su suka cancanta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel