Zanga-zangar Katsina: 'Yan sanda sun kama shugaban CNG

Zanga-zangar Katsina: 'Yan sanda sun kama shugaban CNG

Bayan zanga-zangar lumanar da matasa suka yi sakamakon rashin tsaro da yayi kamari a jihar, jami’an ‘yan sanda sun kama shugaban kungiyar Coalition of Northern Groups (CNG), Nastura Ashir Sharif.

Sharif wanda shine shugaban kwamitin amintattu na Coalition of Northern Groups (CNG) na hannun hedkwatar ‘yan sanda da ke Abuja.

A wata takardar da Tribune Online ta samu daga CNG wacce kakakin kungiyar, Abdulazeez Suleiman yasa hannu, an kama Sharif bayan sun kammala zanga-zangar da suka yi a Katsina a ranar Talata.

Zanga-zangar Katsina: 'Yan sanda sun kama shugaban CNG
Zanga-zangar Katsina: 'Yan sanda sun kama shugaban CNG Hoto: Tribune Online
Asali: UGC

Idan zamu tuna, a ranar Talata, dubban matasa daga jihohin arewa karkashin inuwar CNG suka hadu a Katsina inda suka yi zanga-zanga a kan ta'azzar ayyukan ‘yan bindiga a yankin.

Wannan ce babbar zanga-zanga ta farko da ta tattara matasa daga kungiyoyi masu tarin yawa.

KU KARANTA KUMA: Katsina: 'Yan bindiga sun halaka mutum 5 a kauyen Dan Ali

A baya mun kawo maku cewa dandazon jama’a a jihar Katsina sun fito domin yin zanga-zanga a kan hauhawan rashin tsaro a fadin jihar.

Masu zanga-zangar sun kawar da shingen da jami’an yan sanda suka sanya a manyan tituna yayin gudanar da tattakin nasu, Sahara Reporters ta ruwaito.

A wani sakon murya da majiyar Legit.ng ta samu, an jiyo daya daga cikin jagororin zanga-zangar mai suna Kwamrad Usman Hussaini Rafuka yana fadin cewa:

"Musababbin wannan zanga-zangar da muka shirya, kowa dai ya sani musamman indai mutum yana a yankin arewacin Najeriya, ya san menene musababbin.

“Musababbinta bai wuce yanayin yadda ake kisan al’umma, musamman idan kika dauki jihar Katsina, muna da kananan hukumomi kusan 15 wanda a kullun sai an zub da jini a wannan yankin.

“Da wuya ka ji an ce ba a kashe mutum 20 ba kai har mutum 100 ana kashewa a rana daya.

“Yanzu haka maganar da nake yi da safe akwai wanda yana daga cikin masu wannan zanga-zangar lumanan da muka shirya, wanda da safen nan na kira shi ya batun tafiya sai yake ce mun wallahi yanzu haka a jiya a Batsari akwai wani gari an shiga an tafi da kanin mahaifinsa.

“Wannan ne dalilin da yasa ma ba zai samu halartan zanga-zangar ba. Kin ga kenan shi abun dake faruwa a jihar ya ma shafe shi."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel