Da duminsa: Dakarun Sojin Najeriya sun hallaka yan Boko Haram 13, sun ceto mata da yara 32 (Hotuna)

Da duminsa: Dakarun Sojin Najeriya sun hallaka yan Boko Haram 13, sun ceto mata da yara 32 (Hotuna)

Dakarun sojin Najeriya sun samu gagarumin nasara kan yan ta'addan Boko Haram da kungiyar daular ISWAP a karamar hukumar Gamboru Ngala, jihar Borno, Arewa maso gabashin Najeriya.

Hedkwatar tsaron Najeriya ta sanar da hakan a shafinta na Tuwita da safiyar Laraba, 17 ga watan Yuni, 2020.

Sanarwan ya nuna Sojojin sun hallaka yan ta'addan 13 a kauyukan Kusumu da Warshele da suke boye.

Haka zalika, dakarun sun ceto mata da yara da wasu muggan makamai da bama-bamai daga hannunsu.

Sojojin sun samu nasarar ceto mutane 32; mata 16 da yara 16 daga hannun yan ta'addan.

Da duminsa: Dakarun Sojin Najriya sun hallaka yan Boko Haram 13, sun ceto mata da yara 32 (Hotuna)
Dakarun Sojin Najriya sun hallaka yan Boko Haram 13
Asali: Twitter

Jawabin yace: "Yayinda aka kara kaimin wargaza yan ta'adda a Arewa maso gabas da Arewa maso yamma, yan ta'addan Boko Haram/ISWAP sun saduda yayinda suka gamu da wutan rundunar Operation LAFIYA DOLE"

Da safiya ranar 14 ga Yuni 2020, dakarun sansani na 11 dake karamar hukumar Gamboru Ngala na jihar Borno sun share kauyukan Kusumu da Warshele inda yan ta'addan ke boye kayayyakinsu."

Hakazalika Sojojin sun share garuruwan Kumo, Diime da Sabori inda sukayi artabu da yan Boko Haram. Bayan arangaman, Sojoji sun hallaka yan Boko Haram 13."

KU KARANTA: An sallami dukkan masu cutar Korona a jihar Adamawa

An kwato;

Bindigogin gargajiya 21,

Kananan bindigogi 2,

Bindigan harbi daga nesa 1,

Gurnet 36,

Bam 1

Tutar Boko Haram 2

Sauran sune:

Adduna 5,

Diga 1

Mashi 1

Kekuna 5

Babura 3

Kura 5,

Lasfika 2,

Janareto 1

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel