An sallami dukkan masu cutar Korona a jihar Adamawa

An sallami dukkan masu cutar Korona a jihar Adamawa

Gwamnatin jihar Adamawa ta sallami mutane hudu da suka rage masu fama da cutar Coronavirus dake jihar bayan sun samu cikakken waraka.

Daily Trust ta bada rahoton cewa kwamishanan lafiyan jihar, Farfesa Abdullahi Isa, ya bayyana hakan ne ranar Talata a Yola inda yace babu sauran masu cutar Korona a jihar.

Ya ce gaba daya mutane 42 suka kamu da cutar a jihar tun daga watan Afrilu da ta bulla. Yayinda 38 suka warke, 4 sun rigamu gidan gaskiya.

A cewarsa: "Kwana 54 bayan bullar cutar a jihar Legas, jihar Adamawa ta samu bullar COVID-19 na farko ranar 22 ga Afrilu, 2020."

"A yau, jihar ta gwada mutane 372. Daga ciki 42 suka kamu cutar, ana sauraron sakamakon 19 da suka rage yanzu."

"Duk da cewa kason wadanda suka mutu a jiharmu 9.5% ya wuce na sauran jihohin tarayya dake 2.5%, amma da abin ya wuce haka baccin irin jajircewan da jami'an kiwon lafiya suka nuna wajen kare rayuka."

An sallami dukkan masu cutar Korona a jihar Adamawa
An sallami dukkan masu cutar Korona a jihar Adamawa
Asali: UGC

KU KARANTA: Uwar Jamiyyar APC ta nada Sanata Ajimobi matsayin sabon shugaba

A makonni biyu baya, mun kawo muku jerin jihohi uku da suka sallami dukkan masu fama da cutar Koronansu amma da alamun yanzu jihohi biyu kadai ta rage.

Bayan kimanin mako daya da karewa cugar Korona a jihar Kebbi, hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da samun bullar cutar a jihar Kebbi.

Hakazalika a jihar jihar Sokoto, kwanaki biyu kacal bayan sanar da karewar cutar, an samu karin mutane 12 sabbin kamuwa.

Jihar Zamfara ce wacce ta fara sanar da karewar cutar ranar 28 ga Mayu, 2020 kuma har yanzu ba'a sake samun mai cutar ba.

Kwanaki cutar Korona 100 yanzu a Najeriya kuma an samu akalla mutane 17,148 da suka kamu da cutar. Yayin da mutum 5623 suka warke daga jinyar cutar. Mutum 355 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon annobar da ta zagaye duniya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel