Ba zan iya da jarabarsa ba, tsawon dare babu sassauci - Matar aure mai neman saki

Ba zan iya da jarabarsa ba, tsawon dare babu sassauci - Matar aure mai neman saki

Matashiya mai shekaru 19 a yankin Ndola da ke Zambia ta tsere daga gidan mijinta saboda tsananin bukatar jima'i da mijinta ke yi wanda hakan ke zarcewa tsawon dare.

Matar auren da ke Mushili, ta yi bayanin hakan a gaban wata kotu da ke Kabushi. Ta ce ta tsere daga gidan mijinta saboda ya fiye bukata. Yana ji mata ciwo kuma baya gamsuwa da wuri. Bata bacci don sukan kwashe tsawon dare suna aiki daya.

Charity ta ce mijinta na kwanciya da ita duk dare sannan yana bukatar samfur kala-kala. Hatta lokutan da take al'ada baya sassauta mata.

Ta yi bayanin cewa ba za ta iya jure irin wannan rayuwar ba da zai dinga kwanciya da ita kowacce rana, don haka ta tsere don neman mafita.

An mika shari'ar gaban Majistare Angnes Muswema wacce ke zaman kotun tare da Mildred Namwizye da Evelyn Nalwizya.

"Mijina baya yi sau daya ya hakura, sai yayi da yawa. Ya kan bukaci salon kwanciya kala-kala. Idan nayi kokarin yi masa bayani, sai yace dama hakan ne aure don haka dole a hakura," Lungu tace.

"Ina gajiya sannan ina samun raunika bayan mun gama. Na gaji saboda jarabar tayi yawa. A shirye nake in koma gidansa matukar zai canza kuma ya rage bukatarsa.

Ba zan iya da jarabarsa ba, tsawon dare babu sassauci - Matar aure mai neman saki
Ba zan iya da jarabarsa ba, tsawon dare babu sassauci - Matar aure mai neman saki. Hoto daga The Nation
Asali: Facebook

KU KARANTA: Harin 'yan bindiga: Jama'a ta za su kare kansu idan FG ba za ta iya ba - Sanata

"Idan nayi masa korafi, sai yace idan zan iya cin abinci kowacce rana dole in iya jure jima'i kullum. Baya iya hakura duk tsawon dare," ta jajanta.

Amma Lungu ya ce ya gaji da halin matarsa. Bata mutunta shi tun bayan da ta samu aiki.

Ya sanar da kotun cewa, a lokacin da arzikinsa yayi kasa, ya bata damar neman aiki amma daga nan ta fara rasa lokacinsa. Tana amfani da wannan damar wurin haduwa da samarinta.

Ya ce matarsa na barin gida tare da 'yan uwanta inda suke shan giya a waje. Akwai lokacin da ya taba samun kwaroron roba a jakarta.

"Wata rana na dawo gida da wuri daga wajen aikina amma sai na tarar da matata da wani matashi wanda tace abokinta ne. Na yi kokarin yi mata magana amma ta ki saurarata, saki kawai take so," yace.

Kotun ta amince da sakin sannan ta bukaci mijin da ya biya matar K5,000.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel