Buhari ya nada sabbin sakatarorin dindindin 12 (Sunaye da jihohi)

Buhari ya nada sabbin sakatarorin dindindin 12 (Sunaye da jihohi)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin sabbin sakatarorin dindindin 12 a ma'aikatun gwamnatin tarayya.

Shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya (HoSF), Dr Folasade Yemi-Esan ne ta sanar da hakan a ranar Talata a birnin tarayya Abuja kamar yadda hadimin shugaban kasa Bashir Ahmed ya wallafa a Twitter.

A cewar sanarwar da direktan watsa labarai na ofishin shugaban ma'aikatan tarayya, Mrs Olawunmi Ogunmosunle ta fitar, za a sanar da ranar da za a rantsar da sabbin sakatarorin nan gaba.

Ga sunayen sabbin sakatarorin da jihohin da suka fito kamar haka;

1. Akinlade Oluwatoyin, Kogi

2. Alkali Bashir Nura, Kano

3. Anyanwutaku Adaora lfeoma, Anambra

4. Ardo Babayo Kumo, Gombe

5. Belgore Shuaib Mohammad Lomido, Kwara

6. Ekpa Anthonia Akpabio, Cross River

7. Hussaini Babangida, Jigawa

8. Mahmuda Mamman, Yobe

9. Meribole Emmanuel Chukwuemeka, Abia

1O. Mohammed Aliyu Ganda, Sokoto

11. Tarfa Yerima Peter Adamawa da

12. Udoh Moniloja Omokunmi, Oyo.

DUBA WANNAN: Masoya biyu sun mutu yayin da su ke jima'i na 'kece raini' a otel

A wani rahoton da Legit.ng ta wallafa, kun ji cewa Majalisar wakilan Najeriya ta soki gwamnatin tarayya a kan ikirarin kashe N187 biliyan a kan ciyar da 'yan makaranta.

Kwamitin majalisar da ke kula da baitul Mali ta ga rashin dacewar hakan tare da caccakar shugabar shirin ciyarwar, Temitope Sinkaye.

Shugaban kwamitin, Oluwole Oke, ya kwatanta al'amarin da mara dadi kuma abinda ba zasu lamunta ba.

A saboda haka, kwamitin ta bukaci bayanin yadda shirin ya kashe kudin dalla-dalla.

'Yan majalisar sun matukar fusata da takardun da kwamitin ya bada wanda NICTO ta samu bashin $400 miliyan daga bankin duniya, $321 miliyan daga kudaden Abacha da kuma wata $400 miliyan daga gwamnatin tarayya.

Sikanye ya sanar da kwamitin cewa shirin ciyarwar ya fara tun daga 2016 lokacin da ma'aikatar walwala da jin kan dan kasa ta kirkiro shi kuma ya lamushe N186 biliyan.

Ta ce an kashe N63.2 biliyan a 2018, N32.2 biliyan a 2019 da kuma N124.4 biliyan a 2020.

Mambobin kwamitin sun musanta wannan lissafin saboda hatta mazabunsu basu san da shirin ba.

Ifeanyi Momah daga jihar Anambra karkashin jam'iyyar APGA da Miriam Onuoha daga jihar Imo a karkashin jam'iyyar APC sun yi watsi da wannan rahoton.

Momah ya musanta ikirarin da aka yi na cewa dalibai 200,000 ne suka mora ciyarwar daga karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra inda yake wakilta.

Oke ya ce kwamitin zai duba takardun da aka gabatar amma ya nuna tantamarsa idan majalisar dattawa ce ta fitar da kudin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel