Akwai ingantaccen tsaro, babu 'yan bindiga a jihar Kano - Ganduje

Akwai ingantaccen tsaro, babu 'yan bindiga a jihar Kano - Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ce babu al'amuran 'yan bindigar daji a jiharsa kamar yadda sauran jihohin arewa ke fuskanta.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a jiya yayin tattaunawa da manema labarai a gidan gwamnatin jihar Kano, jaridar Leadership ta ruwaito.

Kamar yadda gwamnan ya sanar, babu ayyukan 'yan bindiga kamar garkuwa da mutane, satar Shanu da kuma hare-haren Boko Haram da sauransu.

Ya danganta tsaro mai inganci da jihar ta samu da yadda ya dage wajen tsaro, hakan ya datse al'amuran 'yan ta'adda a jihar.

"Gwamnatina ta samar da wurin horar da dakarun soji wanda ya lashe miliyoyin naira a Falgore Game Reserve, wanda muka mika ga rundunar sojin Najeriya don hana dukkan 'yan ta'adda zama a dazuzzukanmu," yace.

Akwai ingantaccen tsaro, babu 'yan bindiga a jihar Kano - Ganduje
Akwai ingantaccen tsaro, babu 'yan bindiga a jihar Kano - Ganduje. Hoto daga The Cable
Asali: UGC

KU KARANTA: Zamfara: Matashi ya yi wa matar yayansa fyade daga bisani ya kasheta

A wani labari na daban, kungiyoyi masu zaman kansu a jihar Katsina za su fito zanga-zangar lumana a fadin jihar a ranar Talata don nuna fushinsu ga gwamnatin tarayya da ta jihar sakamakon kashe-kashen da yayi yawa a jihar.

Kwamared Yasin Ibrahim, shugaban kungiyar, ya sanar da jaridar HumAngle a ranar Litinin da dare "Mun shirya yin zanga-zangar Lumana a gobe don nuna bacin ranmu ga hukumomi.

"Mun gano cewa gwamnati bata shirya kawo karshen kashe-kashe, salwantar dukiyoyi da fyade da ake yi wa matanmu, iyayenmu da kannanmu ba.

"Wannan zanga-zangar bata da alaka da siyasa, sako ne mai sauki. Shugaban kasa muke bukatar ya zo ya yi mana gyaran fannin tsaro."

A kalla kungiyoyi 30 ne za su fito wannan zanga-zangar, Ibrahim yace.

Ya kara da cewa: "Mun sanar da cibiyoyin tsaro kuma mun san dokar kasar. Abinda muke bukata daga cibiyoyin tsaro shine hadin kai da kariya.

"A shirye muke don kafa kwamiti na tabbatar da zanga-zangar an yi ta ba tare da wani tashin hankali ba.

"Ina amfani da wannan damar wurin kira ga 'yan jihar Katsina masu kishin kasa da su fito don wannan zanga-zangar saboda ci gaban jiharmu."

Wani mamba a wata kungiya mai zaman kanta wanda ya bukaci a boye sunansa, ya ce "Wannan zanga-zangar da muka shirya za mu yi ta ne don kira ga gwamnati a kan ta kawo karshen abinda ke faruwa a yankinmu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel