Harin 'yan bindiga: Jama'a ta za su kare kansu idan FG ba za ta iya ba - Sanata

Harin 'yan bindiga: Jama'a ta za su kare kansu idan FG ba za ta iya ba - Sanata

Sanata mai wakiltar mazabar Niger ta gabas a majalisar wakilai, Mohammed Sani Musa ya ja kunnen cewa jama'ar mazabarsa a shirye suke da su kare kansu idan gwamnatin tarayya ba za ta iya ba.

Sanata Sani Musa ya sanar da hakan ne yayin martani a kan harin 'yan bindiga na Kundu da Yakila da ke karamar hukumar Rafi ta jihar, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Harin da aka kai ranar Asabar ya yi sanadin mutuwar 'yan sanda hudu, mazauna kauyen masu tarin yawa sun samu rauni sannan anyi garkuwa da wasu.

Dan majalisar ya nuna rashin jin dadinsa a kan yadda gwamnati ta gaza kawo karshen kashe-kashen da ke aukuwa a yankin.

"Zuciyata na kuna ganin yadda jini ke zuba a mazabata. Ana yi wa mata fyade tare da kashesu.

"Ana yi wa maza kisan gilla sannan ana mayar da kananan yara marayu. Wannan al'amarin na matukar tada min da hankali.

"Muna ta kira ga gawamnatin tarayya, mun kai ziyara ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan wannan al'amarin.

"Amma har yanzu babu karshen lamarin don ana ci gaba da kashe mana jama'a," yace.

Harin 'yan bindiga: Jama'a ta za su kare kansu idan FG ba za ta iya ba - Sanata
Harin 'yan bindiga: Jama'a ta za su kare kansu idan FG ba za ta iya ba - Sanata. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Dakarun soji sun harbe kwamandan Boko Haram, Abu Imrana

Sanata Musa ya ce matasan yankin sun yanke shawarar cewa idan ba a yi komai ba, za su kare kansu daga 'yan bindigar dajin.

"Tunda gwamnati ta nuna rashin damuwarta a kan abinda ke damunmu, za mu dauka mataki."

Ya kara yin kira ga gwamnatin tarayya da ta kafa wurin zaman rundunar sojin Najeriya a yankin.

A wani labari na daban, kungiyoyi masu zaman kansu a jihar Katsina za su fito zanga-zangar lumana a fadin jihar a ranar Talata don nuna fushinsu ga gwamnatin tarayya da ta jihar sakamakon kashe-kashen da yayi yawa a jihar.

Kwamared Yasin Ibrahim, shugaban kungiyar, ya sanar da jaridar HumAngle a ranar Litinin da dare "Mun shirya yin zanga-zangar Lumana a gobe don nuna bacin ranmu ga hukumomi.

"Mun gano cewa gwamnati bata shirya kawo karshen kashe-kashe, salwantar dukiyoyi da fyade da ake yi wa matanmu, iyayenmu da kannanmu ba.

"Wannan zanga-zangar bata da alaka da siyasa, sako ne mai sauki. Shugaban kasa muke bukatar ya zo ya yi mana gyaran fannin tsaro."

A kalla kungiyoyi 30 ne za su fito wannan zanga-zangar, Ibrahim yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel