Da sauran kwana: Yan sanda sun ceci matashin da yayi kokarin fadawa kogin 3rd Mainland

Da sauran kwana: Yan sanda sun ceci matashin da yayi kokarin fadawa kogin 3rd Mainland

- Wani fusataccen matashi a jihar Legas ya yi kokarin kashe kansa

- Matashin ya yi kokarin tsundumawa kogin 3rd Mailand amma yan sanda suka ceceshi

- Jami'an hukumar RRS sun garzaya da shi ofishin yan sandan Oworo kuma an tuntubi iyalansa

Allah ya kiyaye wani matashi na da sauran kwana a jihar Legas ranar Litinin, 15 ga watan Yuni, yayinda jami'an hukumar yan sandan RSS suka ceci rayuwarsa yayinda yayi kokarin kashe kansa.

Matashin, wanda ba a bayyana sunansa ba yayi kokarin tsundumawa kogin 3rd Mainland dake jihar Legas saboda ya gaji da rayuwa.

Amma jami'an yan sanda suka galabesa da kalamai da karfi suka cece shi.

Da sauran kwana: Yan sanda sun ceci matashin da yayi kokarin fadawa kogi 3rd Mainland
kogin 3rd Mainland
Asali: Twitter

Matashin sanye da farin kaya da wando mai rusa kasa ya bayyanawa jami'an yan sandan cewa gaba daya ya gaji da rayuwa, abin duniya ya ishe shi.

Bayan haka, jami'an yan sandan sun garzaya da shi ofishin yan sandan Oworo yayinda aka tuntubi iyalansa.

KU KARANTA: Mun fasa bude Masallatai da Majami'u - Gwamnan jihar Legas

Jami'an sun bayyana cewa: "Jiya jajirtattun jami'anmu dake gadar 3rd Mainland sun haa wani matashi daga fadawa cikin kogin."

"Ya bayyana cewa ya gaji da rayuwa ne saboda haka yake son fadawa cikin kogin duk da kokarin hanashi da yan sanda sukayi."

Da sauran kwana: Yan sanda sun ceci matashin da yayi kokarin fadawa kogi 3rd Mainland
3rd Mainland
Asali: Depositphotos

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel