Sallamar daraktar NBET: Ministan kudi da ministan wutar lantarki sun yi 'arangama'

Sallamar daraktar NBET: Ministan kudi da ministan wutar lantarki sun yi 'arangama'

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da wasiku biyu da ke bada umarni mabanbanta ga Marilyn Amobi, manajan daraktar Nigerian Bulk Electricity Trading Company (NBET).

A wata takarda da aka fitar a ranar Litinin, Sale Mamman, ministan wutar lantarki ya bayyana Nnaemeka Ewelukwa a matsayin wanda zai gaji Amobi.

Mamman ya ce ya samu amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin nadin Ewelukwa don shugabantar NBET.

"Zai gaji Marilyn Amobi a matsayin manajan darakta. Tsohuwar manajan daraktan za ta iya ci gaba da hutunta a take," wasikar daga ministan wutar lantarki ta bayyana.

"Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aminta da wannan bukatar."

Amma kuma wasika daga ma'aikatar kudi wacce jaridar The Cable ta gani, ta ce shugaban kasar ya amince da ci gaban aikin Amobi har zuwa lokacin da wa'adin mulkinta zai kare a ranar 24 ga watan Yuli.

Wasikar mai kwanan wata 15 ga Yuni na tare da wata takarda daga Ibrahim Gambari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa.

Sallamar daraktar NBET: Ministan kudi da ministan wutar lantarki sun yi 'arangama'
Sallamar daraktar NBET: Ministan kudi da ministan wutar lantarki sun yi 'arangama'. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Dakarun soji sun harbe kwamandan Boko Haram, Abu Imrana

"Shugaban kasa ya amince a kan Amobi ta ci gaba da aikinta har zuwa wa'adinta ya cika daga nan sai Nnaemeka Eweluka ya karba ragamar. Wa'adin ya fara ne daga ranar 25 ga watan Yulin 2016 kuma zai kare a ranar 24 ga watan Yulin 2020," wasika daga ma'aikatar kudi ta bayyana.

Ganin cewa dukkan wasikun sun samu amincewar shugaban kasa, babu tabbacin wacce wasika ce za a yi amfani da ita.

Da farko dai NBET na ma'aikatar wutar lantarki wacce Sale Mamman ke shugabanta.

Amma kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mayar da cibiyar zuwa ma'aikatar kudi, kasafi da tsarin na kasa bayan Mamman ya yi yunkurin sallamar Amobi a ranar 24 ga watan Disamba.

A wancan lokacin, Mamman ya bukaci Amobi da ta yi murabus sakamakon zargin ta da damfara da aka yi kuma aka kafa kwamitin bincikarta.

Amma kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya soke wannan umarnin tare da mayar da Amobi kujerarta.

A ranar 7 ga watan Mayu, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sauya akalar cibiyar inda ministar kudi, Zainab Ahmed ke jagoranta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel