Dalilin da yasa muka fasa bude Masallatai da Majami'u - Gwamnan jihar Legas

Dalilin da yasa muka fasa bude Masallatai da Majami'u - Gwamnan jihar Legas

Gwamnatin jihar Legas ta sanar da cewa an fasa bude Masallatai da coci-coci da aka yi niyyar budewa ranar 19 ga Yuni saboda karuwar sabbin masu kamuwa da cutar Korona a jihar.

Gwamnan jihar, Babajide Sanwoolu, ya bayyana hakan ne ranar Talata.

A yanzu, jihar Legas ce mafi yawan adadin masu Korona da adadi 7,317.

Gwamnan yace: "Mun dakatad da shirin bude wuraren ibada a jihar Legas har sai wani lokacin kuma."

"Za mu cigaba da lura da lamarin domin yanke shawara saboda kare rayukan dukkanku al'ummar jihar Legas."

"Wannan ba shawara bane da na yanke cikin sauki, kawai yadda abubuwa suka canza ne na karuwar masu kamuwa da cutar da kuma shawarin kwararrun masana kiwon lafiya."

"Saboda haka, dukkan wuraren bauta a jihar Legas za su cigaba da kasancewa a kulle. Hakazalika wuraren bukukuwa, shakatawa da taron kungiyoyi"

Gwamnan ya bayyana ranar Litinin cewa mutane 7,319 suka kamu da cutar a jiharsa.

Daga cikinsu, 1,137 sun samu waraka kuma an sallamesu, yayinda 82 sun mutu.

Yanzu-yanzu: Mun fasa bude Masallatai da Majami'u - Gwamnan jihar Legas
Yanzu-yanzu: Mun fasa bude Masallatai da Majami'u - Gwamnan jihar Legas
Asali: Twitter

Za ku tuna cewa a ranar Alhamis 4 ga Yuni, Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da cewa ya amince da fara bude wuraren bauta daga ranar Juma'a 19 ga Yuni, 2020.

Ya ce za'a fara da Masallatai ne ranar 19 ga Yuni yayinda za'a fara bude coci-coci ranar 21 ga Yuni, 2020.

Gwamnan ya sanar da hakan ne yayinda yake hira da manema labarai a gidan gwamnatin jihar dake Marina.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel