FG ta lissafa sharruda 6 na bude makarantu

FG ta lissafa sharruda 6 na bude makarantu

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayar da sharrudan bude makarantun sakandare da na gaba da sakandare a kasar.

Karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba ne ya bayar da sanarwar sharrudan a ranar Talata a birnin tarayya Abuja.

Ya yi wannan jawabin ne a taron tsare tsare na 2020 a kan matakin daukan dalibai a makarantun gaba da sakandare da hukumar JAMB za ta yi.

FG ta lissafa sharruda 6 na bude makarantu
FG ta lissafa sharruda 6 na bude makarantu. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

Nwajiuba ya lissafa sharrudan kamar haka

1. Ya zama wajibi dukkan makarantu su tanadar da wuraren wanke hannu

2. Samar da naurorin gwada yanayin zafi ko sanyi na jikin dan adam

3. Samar da sinadarin kashe kwayoyin cutar jikin mutum a dukkan kofofin shiga makaranta, ofisoshi, ajujuwa da dakunan kwanan dalibai d.s.

4. Ya zama dole ayi feshin kashe kwayoyin cuta a dukkan harabar makarantu

5. Ya zama dole makarantu su tabbatar da tsafta a koda yaushe

DUBA WANNAN: Masoya biyu sun mutu yayin da su ke jima'i na 'kece raini' a otel

6. Tabbatar da bayar da tazara a ajujuwa da wuraren hada hadan mutane

Kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito, ministan ya yada wa makarantun gaba da sakandare a Najeriya kan matakan da suka dauka na bayar da gudunmuwa wurin yaki da annobar ta korona.

Amma ministan ya yi gargadin cewa kada makarantun su bude ba tare da samun izini daga wurin gwamnatin tarayya ba.

Ya kara da cewa, "A yayin da muke sa ran sassauta dokokin kulle tare da bude makarantun mu, ina kira ga shugabanin makarantun su dakata har sai sun samu umurni daga gwamnati.

"Sannan su fara aiwatar da sharrudan da dokokin da hukumar kiyayye cututtuka masu yaduwa, NCDC, ta shimfida."

Ministan ya kuma yi kira ga iyayen yara su kara hakuri bisa rufe makarantun da gwamnatin tarayya ta yi.

Ya ce gwamnatin ta yi hakan ne domin tabbatar da kiyaye rayuka da lafiyan daliban da malamansu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel