Satar Miliyoyin Naira: Rundunar Soji ta kori Janar Hakeem Otiki
An kori tsohon babban Kwamandan Rundunar Mayakar Sojin Najeriya ta 8 da ke Sokoto watau GOC, Manjo Janar Hakeem Otiki daga aiki.
Kotun wucin gadin da Hukumar Kula da Al'amuran Sojoji ta kafa ne don yi masa shari'a kan sace wasu miliyoyin kudade mallakar rundunar ta yanke hukuncin.
Kotun karkashin jagorancin Laftanat Janar Lamidi Adeosun ta samu tsohon GOC din da laifi kan tuhuma biyar da ake masa.

Asali: UGC
DUBA WANNAN: Masoya biyu sun mutu yayin da su ke jima'i na 'kece raini' a otel
An Otiki ne da satar Naira miliyan 100 da kuma Naira miliyan 160 mallakar rundunar sojojin Najeriya.
An kuma same shi da laifuka biyu na kin bin dokar rundunar soji karkashin sashi na 66 da Armed Forces Act (AFA).
Amma sai Hukumar Kula da Alamuran Sojojin ta amince sannan korar da aka masa za ta tabbata.
Ku biyo mu don karin bayani ...
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng