Harbe-harbe a fadar shugaban kasa: An saki dogarawan Aisha Buhari

Harbe-harbe a fadar shugaban kasa: An saki dogarawan Aisha Buhari

Biyo bayan harbe-harben bindiga da aka yi a fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke birnin Abuja, an tsare wasu dogarawa masu bai wa uwargidan shugaban kasar kariya.

Kwanaki hudu bayan tsare masu tsaron lafiyar Aisha Buhari, babban sufeton 'yan sanda, Muhammad Adamu, ya ba da umarnin a sake su.

An tsare dogarawan tun a ranar Juma'a, 12 ga watan Yuni, biyo bayan harbe-harben da aka yi a fadar shugaban kasa.

Aukuwar wannan lamari ya janyo cece-kuce da bayyana damuwa a kan ko cewa shugaban kasa Buhari ya na cikin hatsari.

Sai dai kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa, fadar shugaban kasa ta bayar da tabbacin cewa, mai rike da akalar jagorancin kasar ya na nan cikin koshin lafiya kuma babu abinda ya same shi.

Fadar shugaban kasa da ke Aso Rock a birnin Abuja
Hakkin mallakar hoto: fadar shugaban kasa
Fadar shugaban kasa da ke Aso Rock a birnin Abuja Hakkin mallakar hoto: fadar shugaban kasa
Asali: Getty Images

Jami'an tsaron masu bai wa uwargidan shugaban kasar kariya da suka shiga hannu sun hadar da babban dogarinta, CSP Usman Shugaba, da DSP Sherrif Kazeem sai kuma wasu jami'ai hudu.

An umarci da su koma gaban hukuma a ranar Talata domin a ci gaba da gudanar da bincike kamar yadda shugaba Buhari ya ba da umarnin a aiwatar.

KARANTA KUMA: Jihohi 35 da cutar korona ta bulla a Najeriya - NCDC

Wani babban jami'in tsaro ne ya tabbatar wa da manema labarai hakan.

Ya ce: "An saki dukkanin dogarawan uwargidan shugaban kasa domin a basu damar komawa gida su wartsake."

"An sake su a ranar Litinin, amma ana sa ran za su dawo don ci gaba da bincike a ranar Talata."

Legit.ng ta ruwaito cewa, wannan rudani ya auku a fadar shugaban kasa tun a ranar Alhamis da daddare tsakanin Aisha da kuma wani hadimin shugaban kasar, Sabi'u Yusuf.

Aisha Buhari da kuma 'ya'yanta uku; Zahra, Halima da Yusuf, sun garzaya har gidan Sabi'u, inda suka nemi ya killace kansa bayan ya yi balaguro zuwa Legas don gudun yada cutar korona.

Sa'insa ta kaure tsakaninsu yayin da Sabi'u wanda aka fi sani da Tunde ya ce babu bukatar ya killace kansa.

Yayin da muhawara ta yi zafi ne dogarawan da suka rako A’isha Buhari suka fara harbi cikin iska, lamarin da ya sa Sabiu Tunde ya ranta a na kare, a cewar rahotanni.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel