Katsina: Jama'a za su fito zanga-zanga a fadin jihar a kan kashe-kashen 'yan bindiga

Katsina: Jama'a za su fito zanga-zanga a fadin jihar a kan kashe-kashen 'yan bindiga

Kungiyoyi masu zaman kansu a jihar Katsina za su fito zanga-zangar lumana a fadin jihar a ranar Talata don nuna fushinsu ga gwamnatin tarayya da ta jihar sakamakon kashe-kashen da yayi yawa a jihar.

Kwamared Yasin Ibrahim, shugaban kungiyar, ya sanar da jaridar HumAngle a ranar Litinin da dare "Mun shirya yin zanga-zangar Lumana a gobe don nuna bacin ranmu ga hukumomi.

"Mun gano cewa gwamnati bata shirya kawo karshen kashe-kashe, salwantar dukiyoyi da fyade da ake yi wa matanmu, iyayenmu da kannanmu ba.

"Wannan zanga-zangar bata da alaka da siyasa, sako ne mai sauki. Shugaban kasa muke bukatar ya zo ya yi mana gyaran fannin tsaro."

A kalla kungiyoyi 30 ne za su fito wannan zanga-zangar, Ibrahim yace.

Ya kara da cewa: "Mun sanar da cibiyoyin tsaro kuma mun san dokar kasar. Abinda muke bukata daga cibiyoyin tsaro shine hadin kai da kariya.

"A shirye muke don kafa kwamiti na tabbatar da zanga-zangar an yi ta ba tare da wani tashin hankali ba.

"Ina amfani da wannan damar wurin kira ga 'yan jihar Katsina masu kishin kasa da su fito don wannan zanga-zangar saboda ci gaban jiharmu."

Katsina: Jama'a za su fito zanga-zanga a fadin jihar a kan kashe-kashen 'yan bindiga
Katsina: Jama'a za su fito zanga-zanga a fadin jihar a kan kashe-kashen 'yan bindiga. Hoto daga HumAngle
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Dakarun soji sun harbe kwamandan Boko Haram, Abu Imrana

Wani mamba a wata kungiya mai zaman kanta wanda ya bukaci a boye sunansa, ya ce "Wannan zanga-zangar da muka shirya za mu yi ta ne don kira ga gwamnati a kan ta kawo karshen abinda ke faruwa a yankinmu.

"Wannan ya zama dole sakamakon halin ko-in-kula da shugaban kasa da gwamna ke nuna mana."

Wasu mazaunan jihar sun ce za su fito zanga-zanga amma sun ja kunnen cewa "Idan ba a dauka mataki a kan kashe-kashe, garkuwa da mutane da fyaden da ake yi wa matanmu a jihar ba, zanga-zanga ta gaba za ta zama irin wacce basu so."

"Muna fatan cewa zuwa karshen zanga-zangar, za su ji kukanmu tare da kawo mana dauki da gaggawa," suka ce.

Usman Sani, daya daga cikin mazauna jihar, ya ce "amfanin wannan zanga-zangar shine tsanantawa gwamnati wurin kawo mana dauki a kan al'amuran 'yan ta'adda."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel