Buhari: Farfesa Ango Abdullahi ya maida martani, ya ce miliyoyi su na tare da shi

Buhari: Farfesa Ango Abdullahi ya maida martani, ya ce miliyoyi su na tare da shi

Yayin da ake fama da kashe-kashe a yankin Arewacin Najeriya, kungiyar Dattawan Arewa ta NEF, ta fito ta yi Allah-wadai da abin da ke faruwa, ta ce gwamnatin kasar ta gaza kare jama’a.

Bayan kungiyar NEF ta bakin Farfesa Ango Abdullahi ta soki kamun ludayin shugaban kasa Muhammadu Buhari, hadimin shugaban kasa Femi Adesina ya fito ya maida mata martani.

Femi Adesina wanda ke magana da yawun bakin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce babu kowa a cikin tafiyar wannan kungiya ta NEF face Ango Abdullahi wanda ke babatun banza.

Sa’o’i kusan 25 da jawabin shugaban kasa ta bakin Femi Adesina, Ango Abdullahi ya sake maida masa martani inda ya ce miliyoyin ‘yan kasa su na tare da shi a kan abin da ya fito ya fada.

Jaridar Vanguard ce ta rahoto raddin da farfesa Ango Abdullahi ya yi wa Adesina, ya ce: “Dakaruna su ne miliyoyin mutanen Najeriya da su ka fito su ka yarda da gazawar sojan da ya ke ikirarin yana da rundunar da za ta tsare kasar.”

Wannan kakkausar magana ta tsohon shugaban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta fito ne a ranar Litinin, 15 ga watan Yuni, 2020.

KU KARANTA: A fadi sunayen Sarakunan da ke tare da 'Yan bindiga - Katsinawa

Buhari: Farfesa Ango Abdullahi ya maida martani, ya ce miliyoyi su na tare da shi
Femi Adesina
Asali: UGC

Bayan jawabin na Farfesa Abdullahi da kungiyar NEF, kiristoci ta kungiyar CAN a jihar Kaduna sun goyi bayan wannan batu, inda su ka ce babu shakka gwamnati ta gaza kawo zaman lafiya.

Ita kuma kungiyar AYCF ta matasan Arewa ta yi kaca-kaca da Femi Adesina a kan sukar Ango Abdullahi da ya yi. Shugaban AYCF, Yerima Shettima, ya bukaci Adesina ya fito ya nemi afuwa.

Kungiyar ta yi tir da yadda hadiman shugaban kasar ya yi watsi da maganar gaskiyar da dattijon ya fadawa gwamnati, sai ya buge da ci masa mutunci, Shettima ya ce ba za su dauki wannan ba.

“Mun gaza gane dalilin da ya sa maganar gaskiya daga bakin Ango Abdullahi game da kashe-kashen da ake yi a Arewa za su jawowa dattawanmu kalamai marasa dadi.”

“Mun yi imani cewa Femi Adesina ba zai taba yin irin wannan kalamai ga dattawan Yarbawa ba.” Don haka ne Yerima Shettima ya nemi Adesina ya janye kalamansa ya bada hakuri.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel