An sake samun dan majalisa da kwamishina da suka kamu da korona a Gombe

An sake samun dan majalisa da kwamishina da suka kamu da korona a Gombe

Kwamitin yaki da COVID-19 da aka fi sani da coronavirus na jihar Gombe ta ce wani jamiin gwamnati da dan majalisar jihar sun kamu da cutar ta korona.

Shugaban kwamitin Farfesa Idris Muhammad ne ya tabbatar da hakan kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A yayin da ya ke sanar da sabbin alkallumar annobar da kwamitin ta saba yi a kullum, Farfesa Muhammad ya ce an yi wa mutum 3,668 gwaji cikinsu guda 410 sun harbu da cutar.

Ya ce kamar jihar Legas, jihar Gombe ita ma ta fara yi wa mutane da yawa gwaji sakamakon samun masu cutar da yawa a jihar.

A baya, an gano yan majalisar jihar biyar da mashawarcin gwamnan jihar na musamman sun kamu da kwayar cutar ta COVID-19.

An sake samun dan majalisa da kwamishina da suka kamu da korona a Gombe
An sake samun dan majalisa da kwamishina da suka kamu da korona a Gombe. Hoto daga Tribune
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Masoya biyu sun mutu yayin da su ke jima'i na 'kece raini' a otel

A baya, majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa kakakin majalisar jihar ta Gombe, Ibrahim Sadiq Abubakar shima ya kamu da mugunyar kwayar cutar ta korona.

A wani labarin daban, kun ji cewa wasu da ake kyautata zaton 'yan bindiga ne a ranar Litinin sun sace a kalla mutum 25 a jihar Zamfara.

Lamarin ya faru ne a garin Bindin da ke karamar hukumar Maru na jihar Zamfara kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

'Yan bindigan da suka kai farmakin sun yi wa garin kawanya ne sannan suka aike da kimanin mutum shida daga cikinsu zuwa cikin garin don aiwatar da abinda suka zo yi.

"Gida gida suke shiga suna zaban mutane. Sun tafi da mutanen cikin daji sun ce iyalansu su biya kudin fansa kafin a sako su.

"Daya daga cikin wadanda suka sace ya yi saa ya tsere sannan sun sako wata mata saboda tana da jariri," inji wani mazaunin garin.

An yi kokarin ji ta bakin Kakakin Rundunar 'Yan sandan jihar, SP Muhammad yayin rubuta wannan rahoton amma hakan ya ci tura.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel