Ambaci sunayen Sarakunan gargajiyan da ke taimakawa yan bindiga a Katsina - An bukaci Garba Shehu

Ambaci sunayen Sarakunan gargajiyan da ke taimakawa yan bindiga a Katsina - An bukaci Garba Shehu

Mutane a jihar Katsina sun bukaci gwamnatin tarayya ta bayyana sunayen sarakunan gargajiyan da ake zargi suna taimakawa yan bindiga wajen kashe al'ummarsu.

Sun ce abin kunya ne idan hukuma ta ki bayyana sunaye da damke sarakunan gargajiyan da aka samu da hannu cikin matsalar rashin tsaron da ya addabi jihar Katsina da sauran jihohin yankin Arewa maso yammacin Najeriya.

Kawo yanzu an yi asaran daruruwan rayuka kuma an kori dubbunai daga muhallansu sakamakon wannan annohar.

Masu unguwa da mazauna yankunan da ake kai wadannan hare-hare sun bayyanawa Daily Trust cewa ya zama wajibi fadar shugaban kasa ta bayana wadanda ke taimakawa yan bindiga domin kawar da zargi.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Dan majalisa ya kamu da COVID-19

Wannan bukata ya biyo bayan bayanin da mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, yayi ranar Litinin.

Ya bayyana cewa akwai sarakunan gargajiya a jihar shugaban kasa Muhammadu Buhari dake daukan nauyin yan bindigan dake kashe al'ummarsu.

Malam Garba Shehu ya bayyana hakan ne ranar Litinin a hirar da yayi a shirin Sunrise Daily na tashar Channels TV.

Ya bayyana cewa wannan dalilin ya sa aka samu tabarbarewar tsaro da kashe-kashe a jihar.

Ambaci sunayen Sarakunan gargajiyan da ke taimakawa yan bindiga a Katsina - An bukaci Garba Shehu
Gwamnan Katsina
Asali: UGC

Yace: "Ba wai muna zargin wani da laifi bane amma maganan gaskiya shine ko a mahaifar shugaban kasa, akwai wasu sarakunan gargajiya da aka kama da hannu cikin hada baki da yan bindiga wajen cutar da al'ummarsu."

"A jihar Zamfara, an kwancewa sarakuna da dakatai rawaninsu. Gaskiyar magana itace akwai masu amfana daga kowani lamarin lalaci."

"A wasu lokutan da suka gabata, hukumar mayakan sama ta ajiye wasu jirage a Katsina, har yanzu suna waje."

"Sun gano cewa jirgin yaki na tashi daga tashar jirgin saman Katsina, kafin ta isa Zamfara domin ragargazansu, an kirasu a waya cewa ga Sojoji nan zuwa, sai su gudu."

"Daga karshe hakan ya tilasta mana tashi daga wurare masu nisa irinsu Kaduna da Kano domin kai hari Zamfara."

A hirar da Daily Trust tayi da wasu mazauna wuraren da rikicin ya shafa a Batsari, Faskari da Dutsinma, sun bayyana cewa gwamnati ta daina boyewa idan akwai gaskiya cikin lamarin kawai ta damke wadanda ake zargi.

Yayinda wasu kuma suna ganin cewa wannan jawabi na iya kara janyo tabarbarewar tsaro a jihar.

Tuni dai gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya nemi afuwar al'ummar jihar saboda ya gaza kare rayukansu.

Da ya ke zantawa da manema labarai a gidan gwamnati a Katsina, Masari ya ce yana bakin ciki saboda tun hawarsa mulki Katsinawa ba su runtsa ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel