Karin mutum 573 sun kamu da korona a Najeriya, jimilla 16,658

Karin mutum 573 sun kamu da korona a Najeriya, jimilla 16,658

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 573 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11.50 na daren ranar Litinin 15 ga Yuni na shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 573 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

Lagos-216

Rivers-103

Oyo-68

Edo-40

Kano-21

Gombe-20

FCT-17

Delta-13

DUBA WANNAN: 'Da yardarsu muke saduwa', inji magidancin da ke zina da 'ya'yansa mata biyu

Plateau-12

Bauchi-12

Niger-10

Kebbi-9

Ogun-8

Ondo-8

Abia-7

Nasarawa-5

Borno-1

Kwara-1

Benue-1

Anambra-1

Alkalluman da hukumar ta dakile cututtukan ta fitar a ranar Litinin 15 ga Yunin shekarar 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar ta korona a kasar 16,658.

An sallami mutum 5,349 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 424.

A wani labarin daban kunji gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da umarnin janye dukkan wani shinge da aka saka a iyakokin shiga jihar tare da bayar da umarnin maye gurbinsu da wasu sabbi don cigaba da tabbatar da dokar hana bulaguro a tsakanin jihohi.

A cikin wani jawabi da Muyiwa Adekeye, mai taimakawa gwamna a bangaren yada labarai da sadarwa, ya fitar, gwamnatin Kaduna ta sanar da dakatar da aikin dukkan kwamitin da aka kafa don tsaron kan iyakokin jihar.

A cewar sanarwar, gwamnati ta dauki wannan mataki ne bisa shawarar da kwamitin yaki da annobar korona a jihar ya bayar.

Daga yanzu, shingen kan hanya da aka yarda dasu sune wadanda aka saka domin tabbatar da dokar takaita zirga-zirga a tsakanin karfe 8:00 na dare zuwa 5:00 na safe, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Gwamnatin ta kara da cewa ta samu rahotannin yadda jami'an tsaro da ke aiki a kan iyakoki suke tatsar kudi a hannun direbobi a wuraren da aka saka shingen hanya, lamarin da mahukunta a jihar Kaduna suka ce yana kara kawo dagulewar al'amura.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel