Da duminsa: Sojojin Nijar sun kawowa yan Sokoto dauki, sun ragargaji yan bindiga

Da duminsa: Sojojin Nijar sun kawowa yan Sokoto dauki, sun ragargaji yan bindiga

Dakarun Sojin kasar Nijar sun hallaka dimbin yan ta'adda a yankin Sabon Birni, wani gari da yan bindiga suka addaba a jihar Sokoto.

Jaridar Humangle ta samu rahoto daga masu shaidar idon gani cewa Sojin Nijar ne suka kai farmaki a Burqusuma, wani kauye dake bangaren Nijar a Sokoto.

Sojojin na Nijar sun hallaka daruruwan yan bindigan ranar Litinin misalin karfe 3:15 na dare, masu idon shaida suka bayyana.

Sun ce Sojin Nijar sun hallaka akalla yan bindiga 100 kuma sun babbaka mabuyarsu dake Burqusuma.

Har yanzu hukumar Sojin kasar Nijar basu yi tsokaci kan harin ba amma Bashar Altine Isa, shugaban kungiyar MSJ da wasu mazauna garin sun tabbatar.

Altine yace: "Sojojin da yawa sun dira cikin dare yayinda yan bindigan ke bacci cikin sansaninsu. Sun afka musu kuma suka kashe 100, suka kona baburansu kuma suka damke wasu."

Ya ce daya daga cikin labarai mai dadi game da harin da aka kwashe awa biyu ana fafatawa shine "damke yan bindigan da mai leken asirinsu, Sarkin Fawa Shago."

"Yanzu haka yana hannun Sojin Nijar."

Wani mazaunin garin mai suna Magaji, ya bayyanawa HumAngle cewa "lokacin da Sojin suka dira, duk guduwa mukayi, wannan ba shi bane karo na farko da Sojin Nijar ke zuwa yankinmu neman yan bindiga."

Da duminsa: Sojojin Nijar sun kawowa yan Sokoto dauki, sun ragargaji yan bindiga
Sokoto
Asali: UGC

Yayinda aka tambayeshi ko sojin sun kashe wani mai farin hula ko lalata dukiyar mutanen garin, Magaji ya bayyana cewa "bayan artabun, wasu yan bindigan sun arce cikin daji da raunuka."

"Saboda haka bamu da masaniya ko akwai masu farin hulan da aka kashe ba, saboda har yanzu muna duba lamarin."

KU KARANTA: Jaririn wata 3 ya sullubo daga hannun mahaifiyarsa a ginin saman Asibiti a Abuja

Karamar hukumar Sabon Birni na da nisan kilomita 175 da birnin Sokoto kuma mazauna sun dade suna fuskantar barazana daga wajen yan bindiga.

A ranar Laraba, 27 ga Mayu, yan bindigan sun hallaka akalla mutane 60 yayinda aka nemi da dama aka rasa a kauyukan karamar hukumar Sabon Birni da Isa na jihar Sokoto.

Majiya sun bayyana cewa Sojojin kasar Nijar na tsare iyakansu da Najeriya ne gudun kada yan ta'addan su yi tunanin shiga kasarsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel