Yanzu-yanzu: Ministan wutar lantarki ya sallami daraktan NBET, ya nada sabo

Yanzu-yanzu: Ministan wutar lantarki ya sallami daraktan NBET, ya nada sabo

Sale Mamman, ministan wutar lantarki, ya umarci Marilyn Amobi da ta zarce da hutunsa a matsayin manajan daraktan Nigerian Bulk Electricity Tradin Company (NBET).

Wannan ne karo na biyu da ministan ya bai wa manajan daraktan wannan umarnin. Na farkon an fara ne a ranar 24 ga watan Disamban 2019, jaridar The Cable ta ruwaito.

Amobi, wanda aka maye gurbinta da babban lauya kuma sakatare Nnaemeka Eweluka, an umarcesta da ta bar ofishinsa a watan Disamban 2019.

Umarnin ya fito ne daga wurin Ministan wutar lantarki, Sale Mamman.

Amma a watan Janairun shekarar 2020, Manjo Janar Muhammadu Buhari ya soke sallamar Ajimobi ta wasikar da ya mika ta hannun sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, inda ya bukaci komawar Amobi matsayinta.

Bayan wannan umarnin, an gano cewa an mayar da NBET zuwa ma'aikatar kudi a maimakon ma'aikatar wutar lantarki.

A ranar Litinin, ministan wutar lantarki ya bada umarnin sallamar Amobi sannan ta mika shugabancin cibiyarta ga sabon darakta.

A yayin magana ta bakin mai bada shawara na musamman ga ministan a bangaren yada labarai, Aaron Artimas, ministan wutar lantarkin ya ce sallamar Amobi na daga cikin gyaran bangaren wutar lantarkin da ake yi.

Kamar yadda takardar ta bayyana, "A ci gaban gyaran bangaren wutar lantarki, ministan wutar lantarki, Sale Mamman na sanar da nadin sabon manajan NBET.

"Shine Dr. Nnaemeka Eweluka, babban lauya kuma sakataren kamfanin. Shine zai gaji Dr. Marilyn Amobi. Ana bukatar tsohuwar manajan daraktan da ta mika ragamar mulki gareshi da gaggawa."

Takardar ta kara da tabbatar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sallamar tare da nadin.

Yanzu-yanzu: Ministan wutar lantarki ya sallami daraktan NBET, ya nada sabo
Yanzu-yanzu: Ministan wutar lantarki ya sallami daraktan NBET, ya nada sabo. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Tattalin arziki: Sanusi II ya yi muhimmin kira ga gwamnatin tarayya, ya yi gagarumin hasashe

A wani labari na daban, dakin karatu na Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta, jihar Ogun, ya sallami ma'aikata sakamakon matsin rayuwar da annobar Covid-19 ta janyo.

Shugaban bangaren kula na dakin karatun, Olanike Ogunleye, a wata wasika da jaridar The Nation ta bayyana, ta ce ci gaban ya faru ne sakamakon illar da annobar korona ta yi wa wurin.

Hukumar dakin karatun ta bayyana cewa, annobar ta sa ba za su iya rike yawan ma'aikatansu ba kamar yadda suka yi a da.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel